Dakarun rundunar ta uku 3 mai suna “Operation Safe Haven (OPSH)”, sun samu nasara wajen kakkaɓe wasu ‘yan bindiga yayin da suka kai wani sumame da suka gudanar a ranar Laraba, 3 ga Yuli, a yankunan Tulus da Hokk da ke ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato, da ke da iyaka da jihar Nasarawa.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar, Manjo Samson Zhakom, ya ce, sojojin sun fatattaki ‘yan bindiga a lokacin da suka kai sumamen yayin da sauran ‘yan bindigar suka tsere cikin daji.
- ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kan Al’ummar Benuwe, Sun Kashe ‘Yansanda 4
- Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Ƙwace Iko Da Jagorancin Ƙaramar Hukuma A Katsina
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta kafa sansani a yankin yayin da ta ke sintiri akan titin d ya hada yankunan biyu domin hana ‘yan ta’adda komawa ko samun mafaka.
A wani labarin kuma rundunar ta ce sun kama wani ɗan bindiga ɗauke da makamai. bayan bincike sun gano yana ɗauke da bindiga kirar AK-47 guda ɗaya da harsashi uku da babur guda daya da wayoyin hannu biyu kirar Tecno da kuma tsabar kuɗi.
Wanda ake zargin da kayayyakin da aka kama a hannunsa suna tsare a hannun hukuma yayin da ake ci gaba da bincike da kokarin cafke sauran abokan aikinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp