Dakarun Operation Hadin Kai da ke Arewa maso Gabas sun kashe ‘yan ta’addar Boko Haram biyar tare da kama daya da ransa a wani samame da suka kai a Jihar Borno.
An tattaro cewa sojojin sun samu nasarar ne a ranar Alhamis yayin da suke samu sahihin bayanan sirri na cewa wasu daga cikin mayakan na tada kayar baya ne daga yankin Arewacin Jihar Borno, inda suka nufi hanyar Mafa.
- Ba Zan Koma APC Ba – Mataimakin Tambuwal
- Zan Magance Rashin Aikin Yin Matasa Da Dala Biliyan 10 – Atiku
Majiyoyin leken asiri sun tabbatarwa da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, cewa sojojin sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton bauna tare da kashe biyar daga cikin ‘yan ta’addan nan take.
Sai dai majiyoyin sun ce an mika dan ta’addan da aka kama ga sojoji domin gudanar da bincike.
A cewar majiyoyin, dakarun sojojin sun mamaye yankin, sannan kuma suna bin sahun sauran ‘yan ta’adda domin gano su tare da kawar da su.