Dakarun sojin Nijeriya sun kashe wasu ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB), biyu dauke da makamai a Karamar Hukumar Orsu a Jihar Imo.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba a Abuja.
Nwachukwu, ya ce sojojin na Bataliyar sojin kasa ta 34, tare da hadin gwiwar sojojin ruwa, sojojin sama da sauran jami’an tsaro sun rufar wa masu laifin a jiya Talata a kan hanyar Eke Ututu-Ihitte Nansa.
Ya ce sojojin sun ci karo da ‘yan ta’addar ne a lokacin da suka kai wani samame a kewayen yankin baki daya.
A cewarsa, ‘yan kungiyar da aka kashe sun dauki matakin harba makamin roka daya a lokacin da sojoji kuma su ka rufar musu har suka zakulo su.
“Gwarazan dakarun ba su ji rauni ba ko daya ba, yayin da wasu bama-bamai da ‘yan ta’addar suka dasa a kasuwar Eke Ututu suka yi bindiga, inda suka lalata wasu shaguna a kasuwar.