Dakarun Operation Hadin Kai sun ceto wata ‘yar Chibok da ta haifi ‘yan tagwaye ‘yan watanni hudu a Jihar Borno.
Sojojin tare da hadin gwiwar rundunar tsaron hadin gwiwa ta CJTF sun gudanar da aikin ne a ranar Alhamis, bayan da suka kai farmaki a yankin Bula Dawo da ke karamar hukumar Bama a Jihar Borno, inda suka kashe wasu mahara da ba a tantance adadinsu ba tare da jikkata wasu da dama.
- An Sake Yin Juyin Mulki A Burkina Faso Bayan Wata 8
- Naja’atu Mohammed: Mace Ta Farko Shugabar Kungiyar Daliban Jami’ar ABU
An tattaro cewa Yana Pogu ta auri daya daga cikin dakarun Boko Haram, wanda ya gudu ya bar matarsa da ‘ya’yansa hudu.
A cewar Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, sojojin sun yi artabu tare da fatattakar ‘yan ta’addan, tare da kawar da da dama daga cikinsu.
“A yayin arangamar, sojoji sun yi nasarar ceto Yana Pogu, ‘yar Chibok, wadda ke ita ce ta 19 a jerin ‘yan matan da suka bace tare da ‘ya’yanta hudu,” in ji majiyar.
“An same ta da wasu tagwaye ‘yan watanni hudu a cikin wani yanayi mara kyau. Wasu daga cikin maharan da suka tsere ma sun yi yunkurin yi wa dakarun nasu kwanton bauna amma yayin da suke aiki da bayanan sirri, sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
“An ceto karin mata a yayin arangamar. An muka su ga dakarun Soji na shiyya ta 21 da ke Bama, domin kula da lafiyarsu,” in ji shi.
A shekarar 2014 ne mayakan Boko Haram suka sace dalibai mata 276 a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno.