Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa dakarun soji da ke sintiri a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun ceto mutane 39 da masu satar mutane suka yi awon gaba da su a wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin.
Sanarwar wacce ke kunshe da bayani kan irin aikin da sojin suka yi, ta bayyana yadda masu satar mutanen suka yi wa manyan titunan jihar kawanya.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, wanda ya sanya wa sanarwa hannu, Samuel Aruwan ya ce dakarun sun gwabza da masu satar mutanen a hanyoyin Kaduna zuwa Abuja da Kaduna zuwa Zaria, inda suka jikkata ‘yan bindiga da dama.
Sai dai wasu rahotanni na daban na nuna cewa wasu tawagar ‘yan bindigan ta farmaki matafiya akan hanyar Abuja zuwa Kaduna a yammacin jiya Litinin ko da ya ke babu bayanin rasa rayuka.