Daga Sulaiman Ibrahim
Hadakar sojoji na Shiyya ta daya ta Operation LAFIYA DOLE da na 402 Special Forces Brigade sun ci gaba da kakkabe duk kauyuka da yankunan da ke hannun ‘yan ta’addan Boko Haram (BHTs) da takwarorinsu (ISWAP) dake garin Chikun Gudu, Kerenoa da kewayesu a karkashin rundunar “TURA TAKAIBANGO”.
Hare-haren suna zuwa ne bisa umarnin da shugaban hafsan sojoji na kasa (COAS) Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya bayar lokacin da ya ziyarci Hedikwatar Operation LAFIYA DOLE dake Borno.
A yayin ziyarar aiki da ya kai DIKWA, COAS ya ba da umarni ga sojoji don ci gaba da kwato garuruwan Marte sannan daga baya a ci gaba da aikin share ‘yan ta’addan dake yankin da sauran kauyukan da ke kusa da su wadanda suka hada da Chikun Gudu, Kerenoa da kewayen su.
Bayan bin umarnin, sojojin sun yi nasarar afkawa garuruwan, sun kuma samu abun da ake bukata. A yayin gwabzawar, sojojin sun ci karo da rundunar ‘yan ta’adda masu yawa, amma sun fatattake su da kashe mafi yawa daga cikin su da kame manyan muggan makamai masu yawa.
COAS ya yaba da kwazon sojojin da ke fagen fama, sannan kuma ya da da karfafa musu gwiwa da su ci gaba da matsawa don tabbatar da cewa yankin an tsabtace shi daga ayyukan miyagun.
Ya kuma umurce su da kada su yi kasa a gwiwa akan sabon farmakin da suke kai wa ‘yan ta’adda masu tayar da kayar baya.