Wasu dakarun sojin kasar Gabon sun bayyana a gidan talabijin din kasar, inda suka bayyana cewa sun karbe mulki daga hannun gwamnatin farar hula a kasar.
Sun ce sun soke sakamakon zaben ranar Asabar da aka gudanar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.
- Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Gabon.
- NIS Ta Bude Ofishin Samar Da Ingantaccen Fasfo A Zariya
Hukumar zaben ta ce Mista Bongo ya samu nasara ne a kasa da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a zaben da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi.
Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalansa suka yi a Gabon.
Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin a ranar Laraba, inda suka sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa “dukkan hukumomin kasar”.
Sun kuma ce sun rufe iyakokin kasar har sai illa masha Allah.
Bayani na tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp