• English
  • Business News
Saturday, June 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojojin DR Congo Sun Daƙile Yunƙurin Juyin Mulki

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
in Manyan Labarai
0
Sojojin DR Congo Sun Daƙile Yunƙurin Juyin Mulki
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sojojin Janhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo sun daƙile wani yunƙurin juyin mulki a kusa da ofishin shugaban ƙasar Felix Tshisekedi da ke birnin Kinshasa a yau Lahadi.Lamarin ya faru ne da sanyin safiya kusa da gidan ministan tattalin arzikin ƙasar Vital Kamerhe da ke yankin Gombe, kusa da ofishin shugaban ƙasar da ke Palais de la Nation.

Janar Sylvain Ekenge da yake magana a gidan talabijin na ƙasar ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile yunƙurin juyin mulkin. Ya bayyana cewa duk masu haɗa baki don kawo tarnaƙi ba za su sake yin wata barazana mai tasiri ba.

  • NDLEA Ta Cafke Mai Ciki Da Kudin Jabu Naira Miliyan 3.2
  • Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 386 Bayan Garkuwa Da Su Shekara 10 A Dajin Sambisa

An bayar da rahoton jin ƙarar harbe-harbe a kusa da Palais de la Nation a lokacin yunƙurin juyin mulkin, a cewar majiyoyi da dama. Sai dai Janar Ekenge bai yi karin bayani kan abubuwan da suka faru ko kuma ainihin waɗanda ke da hannu a lamarin ba.

Kamfanin dillancin labaran na AFP ya yi ƙoƙarin tuntubar majiyoyin hukuma amma ba a samu wata amsa ba. Mutane 3 ne dai aka rawaito sun rasa ransa kawo yanzu kuma an kama wasu da dama ciki har da wasu ƴan ƙasar waje.

Da safiyar yau al’amura sun lafa a birnin Kinshasa, kamar yadda ƴan jaridar AFP suka ruwaito. Tun da farko dai rahotannin kafofin sada zumunta sun bayyana harin da cewa wasu mutane ne ɗauke da makamai suka kai gidan Kamerhe, inda wasu daga cikinsu suka koma Palais de la Nation.

Labarai Masu Nasaba

Shahararren Ɗan Kasuwa Aminu Dantata Ya Rasu

Abubuwan Da Tsofaffin Shugabannin Nijeriya Suka Fuskanta Bayan Barin Mulki

Dama dai tuna masu sharhi suke tunanin zai yi wahala ba a kitsa wani juyin mulkin ba saboda ƙasashen turawa musamman Faransa bata goyon bayan juyin mulkin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: CongoFrancerwanda
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Kori Wani Ɗansanda Da Rage Wa 3 Matsayi Kan Haɗin-baki Wajen Aikata Fashi Da Makami

Next Post

An Kaddamar Da Bikin Nuna Kayayyakin Fasahohin Al’adu Masu Alaka Da Gasar Olympics A Shanghai Na Sin

Related

Shahararren Ɗan Kasuwa Aminu Dantata Ya Rasu
Manyan Labarai

Shahararren Ɗan Kasuwa Aminu Dantata Ya Rasu

5 hours ago
Abubuwan Da Tsofaffin Shugabannin Nijeriya Suka Fuskanta Bayan Barin Mulki
Manyan Labarai

Abubuwan Da Tsofaffin Shugabannin Nijeriya Suka Fuskanta Bayan Barin Mulki

16 hours ago
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka
Manyan Labarai

Ganduje Ya Ajiye Shugabancin Jam’iyyar APC

18 hours ago
Ƴan Majalisa Na Binciken Cibiyoyin Ci Gaban Masana’antu 30 Da Aka Yi Watsi Da Su
Manyan Labarai

Ƴan Majalisa Na Binciken Cibiyoyin Ci Gaban Masana’antu 30 Da Aka Yi Watsi Da Su

23 hours ago
Tinubu Ya Sasanta Wike, Fubara, Da Ƴan Majalisar Ribas
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sasanta Wike, Fubara, Da Ƴan Majalisar Ribas

23 hours ago
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tabbatar Da Kisan Jami’anta A Kaduna Da Neja
Manyan Labarai

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tabbatar Da Kisan Jami’anta A Kaduna Da Neja

1 day ago
Next Post
An Kaddamar Da Bikin Nuna Kayayyakin Fasahohin Al’adu Masu Alaka Da Gasar Olympics A Shanghai Na Sin

An Kaddamar Da Bikin Nuna Kayayyakin Fasahohin Al'adu Masu Alaka Da Gasar Olympics A Shanghai Na Sin

LABARAI MASU NASABA

Za a Binne Ɗantata A Madina, Za Ai Yi Sallar Ga’ibi A Kano

Za a Binne Ɗantata A Madina, Za Ai Yi Sallar Ga’ibi A Kano

June 28, 2025
Me Ya Sa Syria Ta Bari Ana Amfani Da Sararin Samaniyarta Wajen Kai Wa Iran Hari?

Me Ya Sa Syria Ta Bari Ana Amfani Da Sararin Samaniyarta Wajen Kai Wa Iran Hari?

June 28, 2025
Wace Nahiya Ce Ta Fi Iya Ƙwallon Ƙafa Tsakanin Turai Da Kudancin Amurka?

Wace Nahiya Ce Ta Fi Iya Ƙwallon Ƙafa Tsakanin Turai Da Kudancin Amurka?

June 28, 2025
Ƙasashen Afrika 10 Da Suka Fi Girman Kasafin Kudi A 2025

Ƙasashen Afrika 10 Da Suka Fi Girman Kasafin Kudi A 2025

June 28, 2025
Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi Reshen Kaduna Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Matafiya A Filato

Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi Reshen Kaduna Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Matafiya A Filato

June 28, 2025
Shahararren Ɗan Kasuwa Aminu Dantata Ya Rasu

Shahararren Ɗan Kasuwa Aminu Dantata Ya Rasu

June 28, 2025
Hoton Tallan Taliyar Indomie

Indomie Ta Kaddamar Da Shirin Gangamin Abinci Mai Gina Jiki Na ‘Ingantaccen Abinci Domin Nasara’

June 28, 2025
Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su

Sin Na Kokarin Gaggauta Taimakawa Kasashen Afirka Da Kara Hadin Gwiwa Da Su

June 27, 2025
Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva

Sin Da Amurka Sun Tabbatar Da Bayanan Tsarin Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Yayin Tattaunawar Cinikayya A Geneva

June 27, 2025
Sojojin DRC: Ƴan Tawayen M23 Sun Kashe Fararen Hula 17

Sojojin DRC: Ƴan Tawayen M23 Sun Kashe Fararen Hula 17

June 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.