• English
  • Business News
Saturday, July 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masanin Birtaniya: Duniya Ta Amince Da Ci Gaban Da Sin Ta Samu A Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Masanin Birtaniya: Duniya Ta Amince Da Ci Gaban Da Sin Ta Samu A Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Manazari kana shahararren masani na jami’ar Cambridge ta Birtaniya, Martin Jacque ya shedawa wakilin CMG cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin ta samu ci gaba na a zo a gani a fannin tattalin arziki da zaman takewa da sauran wasu bangarori 10, abin da ya samu amincewa daga al’ummar duniya baki daya.

Yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ranar 16 ga watan Satumba, Martin Jacque ya bayyana babbar ma’anar nasarar yaki da talauci da Sin ta samu, wadda ta zamewa sauran kasashe abin koyi. Ya ce:
“A cikin shekarun da suka gabata, Sin ta samu gagarumar nasara wajen yaki da talauci. Abin dake da ma’ana matuka. Kuma ya baiwa duk fadin duniya wani sako cewa, kawar da talauci baki daya a duniya abu ne mai yiwuwa.”

  • Gwamnatin Kasar Sin Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Ta Hanyar Ingiza Samun Wadata Ba Tare Da Barin Kowa A Baya Ba

Yayin da yake tabo maganar kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, ya ce, wannan ra’ayi ya bayyana babban karfi yayin da ake fuskantar sauyin yanayi na daidaita harkokin duniya, kuma ya samar da wata hanya da ta dace wajen samun wadatar al’ummar Bil Adama.

Ya ce: “A ganina, kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya muradun daukacin Bil Adama ne. Dole ne mu hada kanmu saboda ganin manyan sauye-sauyen da muke fuskanta, ta yadda za a samu moriya da ci gaba tare.

A halin yanzu, ana fuskantar sauyin yanayi da sauran wasu kalubale, ba za a iya warware wadannan matsaloli ta hanyar dogaro da karfin wata kasa daya kadai ba, don haka, ya kamata kasashen duniya su hada kansu.

Labarai Masu Nasaba

Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

Kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya ya fidda tafarki mafi dacewa ga samun bunkasuwar duniya cikin hadin kai.” (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Daba Sun Farmaki Mai Taimaka Wa Ganduje Na Musamman A Kano

Next Post

Girman Kan Amurka Ya Sake Fuskantar Koma Baya

Related

Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa
Daga Birnin Sin

Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

10 hours ago
Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

11 hours ago
Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka
Daga Birnin Sin

Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka

13 hours ago
Fahimtar Kyawun Bambance-Bambance Kyakkawar Hanya Ce Ta Wanzar Da Zaman Jituwa A Duniya
Daga Birnin Sin

Fahimtar Kyawun Bambance-Bambance Kyakkawar Hanya Ce Ta Wanzar Da Zaman Jituwa A Duniya

14 hours ago
FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”
Daga Birnin Sin

FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”

15 hours ago
An Fitar Da Sanarwar Beijing Bayan Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adama
Daga Birnin Sin

An Fitar Da Sanarwar Beijing Bayan Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adama

16 hours ago
Next Post
Girman Kan Amurka Ya Sake Fuskantar Koma Baya

Girman Kan Amurka Ya Sake Fuskantar Koma Baya

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma

Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma

July 12, 2025
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

July 12, 2025
Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

July 11, 2025
Hadakar Jam’iyyar ADC Ta Fara Dusashe Karfin PDP A Wasu Jihohin Nijeriya

Hadakar Jam’iyyar ADC Ta Fara Dusashe Karfin PDP A Wasu Jihohin Nijeriya

July 11, 2025
Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

July 11, 2025
Nijeriya Na Fuskantar Siyasa Mara Tabbas —  Peter Obi

2027: Takarar Shugaban Kasa Zan Yi Ba Mataimaki Ba – Peter Obi

July 11, 2025
“Sin Daya Tak A Duniya”, Matsaya Ce Da Al’ummun Duniya Suka Kafe Kai Da Fata a Kai

“Sin Daya Tak A Duniya”, Matsaya Ce Da Al’ummun Duniya Suka Kafe Kai Da Fata a Kai

July 11, 2025
2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci A Kawo Karshen Matsalar Sayen Kuri’a

2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci A Kawo Karshen Matsalar Sayen Kuri’a

July 11, 2025
Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka

July 11, 2025
Fahimtar Kyawun Bambance-Bambance Kyakkawar Hanya Ce Ta Wanzar Da Zaman Jituwa A Duniya

Fahimtar Kyawun Bambance-Bambance Kyakkawar Hanya Ce Ta Wanzar Da Zaman Jituwa A Duniya

July 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.