Daga Mahdi M. Muhammad,
Rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF), bangaren dakarun ‘Operation LAFIYA DOLE’ ta lalata akalla motocin bindiga 2 na ‘yan ta’addan Boko Haram, tare da kakkabe wasu da dama daga cikin mayakansu a hanyar Wamdeo-Chul na yankin Kudancin jihar Borno.
Jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu cikin makon nan, a inda yake cewa, an cimma wannan nasarar ne a ranar, 5 ga Janairun 2021, yayin da dakarun suka hada hannu da jiragen yaki masu saukar ungulu na NAF don basu tallafi ta sama yayin da suke kokarin fatattakar ‘yan ta’addan, wadanda suka yi yunkurin keta wuraren 2.
Da suka ga jiragen yaki masu saukar ungulu na NAF din, sai ‘yan ta’addan suka hau kan motocin bindigarsu da babura suka yi kokarin tsarewa da hanzari yayin da suke ta harbin jiragen NAF din. Duk da haka, sai da jiragen NAF din suka buge su da roka na bom, wanda hakan ya kai ga kawar da 2 daga cikin motocin bindigogin ‘yan ta’addan, wanda kuma aka ga daya daga cikinsu yana ci da wuta.