Gidan talabiji na AIT da Raypower sun ce yanzu haka suna ta kokarin yadda za su sulhunta da Hukumar Kula Da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC), domin shawo kan umarnin soke lasisinsu da hukumar ta bayar.
NBC dai ta soke lasisi tashoshin watsa labarai guda 52 ciki har da AIT da Raypower ne bayan samunsu da laifin karya dokar kin sake sabunta lasisinsu.
Darakta-Janar na hukumar, Balarabe Shehu Ilale, ne ya sanar da hakan a ganawarsa da ‘yan jarida a Abuja, yana mai cewa muddin kafafen suka gaza biyan basukan da ake binsu cikin awa 24 to za su fuskanci kwace lasisin gudanarwa na gaba daya.
Sai dai edita a kamfanin DAAR Communications masu mallakin AIT da Raypower, Terverr Tyav ya shaida cewar yanzu haka suna kokarin tattaunawa da NBC domin shawo lamarin, don haka ne ya nemi masu kallo da sauraron kafafen biyu da cewa su kwantar da hankalinsu za a shawo kan matsalar.
Tyav a wani rahoton da ita kanta kafar AIT ta wallafa a shafinta na yanar gizo ta nakalto shi na cewa za su shawo kan matsalar nan kusa.