Idris Aliyu Daudawa" />

Solomon Dalung Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Hatsari A Garin Gombe

An samu hadari wanda ya shafi motar’yan rakiyar  Ministan Matasa da wasanni Solomon Dalung, wadda kuma yayi sanadiyar mutuwar  mutum daya, yayin da kuma mutane 20 suka samu raunuka ban daban.

Daga cikin wadanda suka samu raunuka shi ne mai rikon mukamin shugaban kungiyar matasa ta kasa, Chinedu Mayor.

Mai rikon mukamin shugaban kungiyar matasa ta kasa Comrade Chinedu Enujeko Mayor

Sunday Jika wanda shi ne mai kula da jihar Gombe, yana kuma daga wani sashe ne na bangaren tsaro, yana daga cikin wadanda suke rakiyar Ministan, ya tabbatar daaukuwar hadarin ga manema labarai, ranar Asabar a Gombe.

‘’Mun tarbo Ministan daga filin jirgin sama, akan hanyar mu ta zuwa cikin gari, sai motar Peugeot 406, ta shiga motar da take ma Minista rakiya, ta bugi motar Pilot,

‘’Motar Peugeot ta kama da wuta, amma mun samu damar fito da mutane uku, amma shi direban ya kone cikin motar.

A cikin motar  bus da take cikinn wadanda ke rakiyar Ministan,ita ma mum yoi sa’ar fitowa da mutane, dukkan mutanen da suka samu raunuka, ai kais u asbitin kwararru na Gombe, da kuma asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya. Wakilin kamfanin dillancin labarai na Nijeriya wanda ya je asibitin kwararru da kuma asibitin koyarwa na, ya da likitoci sunma kulawa da wadanda suka samu raunuka, a bangaren kulawa da wadanda suka samu raunuka lokacin hadari.

Lokacin da aka tuntube ta mataimakiyar shugaban asibitin gwamnatin tarayya na Gombe, Dokta Zainab Kaltungo, bata yarda, tayi wani bayani ba, akan halin da ake ciki, yayin da shi kuma shugaban kulawa na Hukumar kiyaye hadura ta kasa Godwin Omiko  ya bayyana cewar, shi yar zuwa lokaci ba a sanar da shi halin da ake ciki ba.

 

Exit mobile version