Connect with us

RAHOTANNI

SSANU Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Gaggauta Aiki Da Sabon Tsarin Albashi

Published

on

Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’in kasarnan, (SSANU), ta gargadi gwamnatin tarayya da kar ta sake ta kure hakurin ma’aikatan kasar nan kan abin da suka kira da rikon sakainar kashin da gwamnatin ke wa batun sabon tsarin albashi. Kungiyar ta ce, matukar gwamnatin ta ci gaba da jan kafa kan batun, tabbas sakamakon ba zai yi mata kyau ba.

Kungiyar ta yi wannan maganan ne bayan kare taron shugabannin ta na 34, wanda suka yi a Jami’ar Jihar Delta, da ke Abraka. Shugaban kungiyar, Kwamred Samson Chijioke Ugwoke, yace, sam gwamnatin tarayya ba ta nu na da gaske take ba kan batun na sabon tsarin albashi duk da alkawurran da ta yi ta yi.

Ya ce, “Mun gargadi gwamnatin tarayya da kar ta sake ta kai ma’aikatan kasarnan makura. A duk lokacin da aka yi maganan abin da ya shafi jin dadin ma’aikata sai ka ga gwamnati tana ta nokewa, amma da zaran lokacin zabe ya zo, nan da nan sai su fito da kudi suna sayen kuri’u.”

Kungiyar kuma ta yi tir da yadda sashen gwamnati ke yin amfani da jami’an tsaro wajen tursasawa sashen majalisa, ta bayyana hakan da barazana ga tsarin dimokuradiyya.

Ya kuma shawarci sashen gwamnati da ta kasance mai girmama dokokin kasa, su kuma rika bin umurnin hukuncin kotu.

Kan batun babban zaben 2019, Ugwoke yace, irin yadda ‘yan siyasa suke tafiyar da harkokin su a halin yanzun, lamarin yana da ban tsoro, ya kuma kirayi ‘yan siyasan da su rika bin ka’idojin kamfen da na zabe domin gujewa dawowan Sojoji kan karagar mulkin kasarnan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: