Ƙungiyar ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya (SSANU) ta sake zaɓar Comrade Mohammed Haruna Ibrahim a matsayin shugaba na ƙasa karo na biyu na shekaru hudu. A zaɓen da aka gudanar a taron wakilainta karo na uku a Abuja, Comrade Ibrahim ya samu nasara da ƙuri’u 842, inda ya doke abokin hamayyarsa, Shishi Luper, wanda ya samu kuri’u 88.
Haka kuma, an yi gasa mai zafi a wasu muhimman muƙamai na ƙungiyar. Dr. Leku Ador ya lashe kujerar mataimakin shugaba da ƙuri’u 611, inda ya doke Dr. Aniete Ati wanda ya samu ƙuri’u 320. A Jami’ar Fasaha ta tarayya Owerri (FUTO), Comrade Uchenna Nwokeji ya samu nasara da ƙuri’u 617 kan Comrade John Igboke, wanda ya samu ƙuri’u 311.
- Daga Gobe Litinin, Ma’aikatan Jami’a Zasu Fara Yajin Aiki
- Kungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’i SSANU Da NASU Sun Janye Yajin Aikin Gargadi Da Suka Shiga
Da yake godiya bayan nasararsa, Comrade Ibrahim ya bayyana sake zaɓarsa a matsayin amanna da kuma sahale masa ci gaba da aiki. Ya bayyana nasarorin da ƙungiyar ta samu a wa’adinsa na farko, musamman a bangaren inganta jin daɗin ma’aikata da kuma kafa tubalin samar wa da ƙungiyar kuɗi ta hanyar manyan ayyuka ba tare da ƙarin kuɗaɗe daga rassan ƙungiyar ba.
Comrade Ibrahim ya yi alƙawarin ci gaba da jagoranci na gaskiya, da ƙarfafa haɗin kai a cikin ƙungiyar, da kuma mayar da hankali kan jin daɗin dukkan mambobi. Ya ce nan ba da jimawa ba za a ƙaddamar da katafaren otal da ƙungiyar ta gina, yana mai jaddada sadaukarwarsa ga makomar SSANU tare da yi wa mambobi alƙawarin jagoranci da sauraron kokensu, da ci gaba da aiki, da kuma haɗin kai.