Zuwa yanzu kananan hukumomi goma sha daya daga cikin 18 da suke fama da matsanancin rashin tsaro sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da aka shafe shekara da shekaru ana yi suka kulla yarjejeniyar zaman sulhu da barayin daji.
Kananan hukumomin sun hada da Jibia da Batsari da Safana da Danmusa da Kurfi da Musawa da Matazu da Faskari da Kankara da Sabuwa da kuma Dandume inda yanzu ake sa ran Dutsinma zata bi sahu.
- Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
- Saliba Ya Sabunta Kwantiraginsa Da Arsenal Har Tsawon Shekaru 5
Sulhu da barayin daji da ake cigaba da aiwatarwa a jihar Katsina Na cigaba da haifar da muhawara a tsakanin masana da kuma sauran al’umma.
Maganganun da ke fitowa daga al’ummar da wannan matsala ta shafa shi ne, su wannan sulhu ya zama alheri gare su, kuma suna fatan cewa hakan za ta dore.
A gefe guda kuma masana na cewa idan har za a yi sulhu da barayin daji kuma a kyalesu da makamai, to akwai sake wai an dafa kaza an ba mai ita kai…
Wanda duk zai gaya maka gaskiya musamman wanda yake zaune ko ya ke zuwa wuraren da aka samu matsalar tsaro a wasu kananan hukumomi na jihar Katsina zai fada maka cewar an samu zaman lafiya fiye da lokutan baya.
An sha ruwaito wadanda wannan bala’i ya shafa suna maida martani ga masu suka sulhu da cewa duk wanda baya goyon bayan wannan sulhu dan ba a wannan yanki yake da zama ba.
Sai dai kuma yin sulhu da barayin daji ba yana nufin an samu zaman lafiya dari-bisa-dari ba. Ana dai samun saukin kai hare-haren ‘yan bindigar amma ba wai an daina ba ne baki daya.
To, ta ya ya al’umma za su amfana da wannan yarjejeniyar zaman sulhu da barayin daji, ana iya cewa hakan zai taimaka ta wajen huldar kasuwancin kiwo da kuma noma da ya fara zama tarihi a wasu wurare da ake wannan ta’addanci.
Idan aka duba salon da barayin daji suke amfani da shi bayan kaddamar da yarjejeniyar zaman sulhu shi ne, duk karamar hukumar da aka wannan sulhu to za su rage kai hare-hare Sannan za su sako wadanda suke tsare da su.
Haka kuma su kan kai hari ne a sauran kananan hukumomin da ba a kulla wannan yarjejeniya ta zaman lafiya da su ba, su yi barna su yi kisa su kwashe kayayyakin da jama’a.
Irin haka na ci gaba da faruwa, misali an yi zaman sulhu da barayin daji a karamar hukumar Kankara amma a satin da ya gabata rahotanni sun bayyana cewa an je an sace mutum 60 a garin Zango da Kankara.
Haka abin yake a karamar hukumar Faskari inda suka je garin Tafoki suka kwashe mashinan jama’a a ya yin da suke cikin gona suna aiki.
Sannan abubuwan da suka bayyana shine ana cigaba da kai hare-hare jefi-jefi kuma ana cigaba da satar jama’a da neman kudin fansa tare da sauran abubuwa marasa dad’i.
A bangaren barayin daji kuwa tuni harkoki suka fara kankama inda yanzu haka suke shigowa gari cin kasuwa da zuwa asibiti domin neman lafiyar su da ta iyalan su.
Ita ma gwamnatin jihar Katsina ta bada tabbacin cewa zata tallafawa wadanda wannan iftila’i ya shafa da jari da makarantu da asibitoci da sauran kayayyakin more rayuwa.
Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya jaddada cewa hatta ‘yan bindigar da suka rungumi zaman lafiya za a taimaka masu da jari domin yin sana’a da za su dogara da kan su.
Gwamnan dai ya sha soka akan yadda rana tsaka ya yi mi’ara koma baya akan matsayar da ta cewa ba zai taba yin sulhu da barayin daji ba, sai dai idan ‘yan bindigar suka sha wuta suka mika kai.
Haka kuma daya daga hadiman gwamna Radda Jamilu Isma’il Mabai ya bayyana cewa ‘yan bindiga ne da kan su suka sha wuta daga jami’an tsaro suka nemi ayi sulhun ba gwamnati ba ce.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp