Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gargaɗi shugabanni da hukumomin tsaro da su guji tattaunawa da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai idan har za a bar su da makaman nasu, yana mai cewa irin wannan salon sulhu ba ya kawo zaman lafiya, sai dai ya ƙara tashin hankali tare da raunana ikon gwamnati.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a matsayin babban baƙo mai gabatar da lacca ga mahalarta taron Executive Intelligence Management Course (EIMC) na 18 a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa (NISS) da ke Abuja, ranar Laraba.
- COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa
- Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, taken laccar shi ne: “Rawar ’Yan Faɗa-da-Gwamnati a Harkokin Tsaro: Ƙalubale da Damar Zaman Lafiya da Ci Gaban Afrika – Salon Zamfara.”
An bayyana cewa mahalartan EIMC 18 sun fito ne daga hukumomin tsaron Nijeriya da kuma ƙasashen Afrika kamar Chadi, Ghana, Rwanda, Somalia, da Gambiya.
A cikin laccarsa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa salon Zamfara ta zama abin koyi ga sauran sassan Afrika wajen nazarin yadda ake ƙoƙarin samar da zaman lafiya da ci gaba.
Ya ce, “A cikin shekaru 20 da suka wuce, tsarin tsaro a Afrika ya sauya sosai. Ra’ayin cewa gwamnati ita kaɗai ke da ikon amfani da ƙarfi yanzu ya fara fuskantar kalubale daga ƙungiyoyi marasa bin tsarin gwamnati – ciki har da ‘yan sa-kai, ƙungiyoyin kare kai, ‘yan ta’adda, barayin daji da kuma cibiyoyin aikata laifuka na ƙasa da ƙasa.”
Gwamnan ya bayyana cewa matsalolin tsaro a Zamfara sun samo asali ne daga rashin aikin yi, taƙaddamar albarkatun ƙasa, da canjin yanayi, tare da yawaitar makamai daga rikice-rikicen yankuna.
Ya ce, tun da suka hau mulki a 2023, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen kafa tsaro bisa ginshiƙai uku:
1. Haɗin gwiwar hukumomin tsaro ƙarƙashin kwamitin tsaro na jiha da gwamnan kansa ke jagoranta.
2. Ƙirƙirar Rundunar Kare Al’umma ta ‘Community Protection Guards’ (CPG) domin tallafawa jami’an tsaro.
3. Haɗa kai tsakanin sarakunan gargajiya, ƙananan hukumomi da hukumomin tsaro wajen raba bayanan sirri da saurin ɗaukar mataki kan barazanar tsaro.
Ya ƙara da cewa, an kafa kwamitocin sulhu a kowace ƙaramar hukuma da suka haɗa da sarakuna, malamai, mata da matasa domin sulhunta rikice-rikice da gina aminci.
Gwamnan ya ce, Zamfara na aiki tare da ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa da kuma ƙasashen ƙetare kamar Kolombiya wajen shirin Preventing and Countering Violent Extremism (PCVE) — wanda ke mayar da hankali kan shirin gyarawa da dawo da masu tubabbun ‘yan ta’adda cikin al’umma.
A cewarsa, “Tattaunawar sulhu na iya taimaka wajen magance rikici, amma zaman lafiya na gaskiya ba zai samu ba sai an ajiye makamai. Sulhu ba tare da iko ba dai-dai yake da miƙa wuya gare su. Barin masu bindiga da makamai yayin da ake tsara sharuɗɗan zaman lafiya hanya ce ta sake janyo tashin hankali.”
Gwamna Lawal ya jaddada cewa duk wani yunƙurin sulhu dole ne ya zama mai tsari, ƙarƙashin jagorancin gwamnati, tare da cikakken iko na doka. “Zaman lafiya na gaskiya yana samuwa ne idan masu ɗauke da makamai sun amince da mulkin doka, kuma gwamnati ta tabbatar tana da ƙarfin kare jama’arta.”
A nasa jawabin, Kwamandan Cibiyar Tsaro ta Ƙasa, J.O. Odama (FSI+, FDC), ya yaba wa Gwamna Lawal bisa hangen nesan da ya gabatar, yana mai cewa, “Ya kawo mana cikakken haske kan gaskiyar lamura a Zamfara. Na tashi a can, na san irin ƙalubalen da ya fuskanta kafin ya zama gwamna. Amma yanzu ya sauya fasalin jihar daga fuskar rashin tsaro zuwa canjin na gaskiya da kyakkyawan fata ga al’umma.”














