Tsohon gwamman Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce zama teburin sulhu da yan bindiga ne hanyar da ta fi dacewa na kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi yankin arewa maso yammacin Nijeriya.
Wata tattaunawa da Sanata Yerima ya yi da BBC, ya bayyana cewa, irin zama teburin sulhu da gwamnatin tarayya ta yi da ‘Yan Neja Delta a kudancin Nijeriya, idan aka bi irin tsarin, za a iya shawo kan matsalar tsaron a yankin arewa maso yammaci.
Sanata Ahmad Sani Yerima tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne kuma Jiharsa na daya daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp