Maganar sulhu da bbarayin daji a Jihar Katsina y afara haifar da da mai ido, abin da Bahaushe ke cewa abu kamar wasa karamar magana ta zama babba.
A bayan dai gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ta ce matsayarta kan batun sunlhu da ‘yan bindiga sun yi hannun riga.
To sai dai, wannan batu fa a Katsina yanzu ba haka yake ba, domin kuwa al’ummomin da suka yanke shawarar yin sulhu da ‘yan ta’adda domin su zauna lafiya, suna cin amfanin hakan.
A yayin da matsayar gwamnati ke cin karo da wannan sulhu, an sha ruwaito cewa Gwamnan Radda yana cewa babu wata hanya da yake ganin zai iya yin sulhu da dan ta’adda, sai dai dan ta’adda ne ya ji wuta daga jami’an tsaro ya mika kansa kuma ya yarda a zauna lafiya.
Zuwa yanzu dai kananan hukumomi guda bakwai ne suka shiga sulhu da barayin daji domin neman tsira da ransu da kuma ci gaba da yin hidimominsu na yau da kullum.
Karamar karamar hukumar Jibiya ita ce ta fara shirya taro domin yin sulhu da ‘yan bindigar, sai dai kuma ba a ga wakilin gwamnatin Jihar Katsina a wannan sulhu ba, amma dai an ga shugaban karamar hukumar da sauran jami’an tsaro da ake zargin daga Abuja suke halartar irin wannan taro.
An yi wannan sulhu a karamar hukumar Jibiya kimanin wata hudu da suka gabata, kuma al’amurra na ci gaba da tafiya yadda ake so, zuwa yanzu dai al’ummomi a wannan karamar hukumar na ci gaba da harkokinsu kamar ba a yi tashin hankalin ‘yan bindiga ba.
Kar a manta duk lokacin da aka yi irin wannan taro gwamnatin Jihar Katsina na cewa babu hannunta kuma ba da ita aka yi sulhu ba, amma dai maganar jama’a na jin ta ne kamar abin nan ake cewa ihu bayan hari.
Karamar hukuma ta biyu da ita ma ta shiga sulhu da barayin daji ita ce, karamar hukumar Batsari, wanda ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga kamar ba gobe, an yi asarar rayuka da duniyoyi, amma yanzu sakamakon wannan zaman sulhu da aka shirya tsakanin al’ummomi da ‘yan bindigar abin ya yi sauki sosai.
Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Hon. Nasiru Mu’azu Danmusa a kullum yana fada wa ‘yan jarida cewa babu ruwan gwamnatin Jihar Katsina da wancan sulhu, shi ne ya tabbatar da cewa idan aka je babbar asibitin Batsari za a ga ‘yan bindiga suna kwanshe suna karbar magani sakamakon cututtukan da suka dame su.
Ita ma karamar hukumar Danmusa ta sha fama da matsalar ‘yan bindiga sakamakon dukkan su suna makwabtaka da babban dajin Rugu da ke da iyaka da Jihar Zamfara, an yi dauki ba dadi a wannan karamar hukuma da barayin daji da al’umma da kuma jami’an tsaro.
Yanzu wadannan kananan hukumomi guda uku da aka ambata sun samu salama sun fara dawowa cikin hayyacin su, inda a yanzu kasuwanni suna cikar farin dango an fara tafiye-tafiye da daddare duk da cewa ana samun kai hare-hare jefi-jefi.
Wannan batun sulhu har gobe yana ci gaba da dore kan masana, musamman wadanda suke da ra’ayin cewa ka da a yi sulhu da barayin daji kuma suke goyon bayan matsayar gwamnatin Radda.
Babban abin da ke dore kan masana da sauran al’umma shi ne, irin yadda gwamnati ke tinkaho da zaman lafiyar da aka samu a wadannan kananan hukumomi duk da ta cewa ba ruwan ta da wannan sulhu, wani lokaci har ikirarin cewa duk wanda ya saba alkawarin da aka yi da shi ba za ta kyale shi ba.
Rahotanni sun bayyana cewa duk wuraren da aka shirya wannan zaman sulhu bana an yi noma sosai, daman barayin daji ne suka hana noman a wadannan yankuna.
Da yawa daga cikin manoma da ‘yan kasuwa da direbobin da aka tattauna da su sun bayyana cewa lallai zaman lafiya na dawowa sannu a hankali duk da cewa wani lokaci ana da fargabar dawowa wannan hare-hare.
Yanzu dai abubuwan da suka bayyana shi ne, sakamakon wannan yarjejeniya da aka kulla da al’ummomi da barayin daji ana samun saukin kai hare-haren ‘yan bindiga, sai dai ba wai an daina kai harin bane baki daya ba, ana samun rahotanni kai hare-haren ‘yan bindiga jefi-jefi.
Masana da masu sharhi kan harkokin tsaro na jin tsoron wannan sulhu da aka ce al’umma ce da kanta ta shirya ba hannun gwamanti a ciki, daga cikin abubuwan da masana ke fargaba shi ne, barayin daji suna rike da makamansu, kuma ba a bayyane cewa an ba su kudi ba, me zai faru idan suna bukatar kudaden kashewa idan bukata ta taso masu?
Abin jira a gani shi ne, yadda wannan yarjejeniya za ta ci gaba da haifar da da mai ido ko akasin haka. Allah ya kyauta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp