Daga Rabi’u Ali Indabawa
A jiya Alhamis ne kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP, karkashin jagorancin Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya samu nasarar sulhunta rashin jituwar dake tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar na Jihar Borno.
Rashin jituwar dai ta samo asali ne yayin da aka samu bangarori biyu masu ikirarin kowannensu ne ya lashe zaben shugaban jam’iyya da aka gudanar a shekarar 2017.
Wannan sabanin ya janyo wa jam’iyyar PDP asara mai tarin yawa a zaben shekarar 2019, wanda hakan ya ba jam’iyyar APC ikon samun jihar a sama.
Bayan Kwamitin Sulhu karkashin jagorancin Dr. Abubakar Bukola Saraki ya gudanar da zama mabambanta guda biyu tare da wadannan bangarorin; a jiya ne aka cimma a gaban dukkanin bangarorin.
Haka kuma kafin cimma wannan matsaya ta sulhu, rikicin nasu sai da ya kai ga kotu har zuwa kotun koli ta Nijeriya. Inda kotu ta bayyana
Dukkanin bangarori na masu ruwa da tsakin na PDP daga Jihar Borno sun gabatar da jawabai na irin hangen da suke da shi kan wannan matsala. Wanda kuma bayan saurarensu ne, sauran membobin kwamitin na sulhu suka tofa albarkacin bakinsu. Inda Sanata Sulaiman Nazif ya yi musu nasiha kan ‘yan uwantaka da yin aiki tare.
A nashi jawabin, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya yi matukar murna da samun sulhu a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar na Jihar Borno. Inda ya ce: “Tabbas wannan nasarar da PDP ta samu a Jihar Borno nasara ce gagaruma, domin kuwa hakan na nuni da cewa PDP za ta kwace yankin Arewa Maso Gabas.
“Ina farin ciki da wannan sulhu da aka samu. Sannan kuma ina godiya ga membobin kwamitinmu na sulhu da dattawa da masu ruwa da tsakin da suka halarci wannan taro.
“Abin karin murna shi ne, sabon shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Borno ya yi alkawarin cewa zai tafi tare da dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar domin a kai ga nasara. Wannan abin murna ne garemu.” Inji shi