Connect with us

RIGAR 'YANCI

Ta’addanci: Kananan Hukumomin Jihar Katsina Sun Dage Addu’o’in Neman Sauki

Published

on

A halin da ake ciki kuma an shirya wata addu’a ta mussamman a kananan hukumomin Faskari da Dandume da Bakori a shiyyar Funtua domin neman dauki ga madaukakin sarki Allah akan kalubalen tsaron da ake fama dashi a wasu sassan jihar nan.

Gwamnatin jihar Katsina tace ta shirya taron addu’ar domin nuna godiya ga Allah game da baiwa iri daban-daban day a yima wannan jiha cikin shekaru aru-aru, daga bangaren mutanen da sukayi fice da kuma albarkatun kasa.

A jawabansu gabanin fara addu’ar daraktocin sashen kudi da mulki a kananan hukumomin Fasakri da Dandume, sun yaba da hangen nesan gwamnati mai ci yanzu akan shirya addu’o’in daidai lokacin bikin babbar sallah.

Alh. Ibrahim Lawal Dan mummini da Alh. Ahmed Idris Mashi sun nuna cewa a halin yanzu da aka samu kai, addu’ar ce kawai mafita a wannan jiha dama kasa baki daya.

Can kuwa a kananan hukumomin Sabuwa da Bakori, shugabannin sashen kudi da mulkin Alh. Sani Labo da Abba Magaji Ingawa kira sukai ga mutanen yanki das u kauracewa aikata duk wani nau’in laifi dake jawo hushin Allah Mahalicci.

Kazalika sun yaba ma gwamnatin jihar Katsina akan bada muhimmaci ga addu’ar dake zama mafita da yanayin da aka samu kai a jiha dama kasa baki daya.

Wakilin Sarkin Yamma Malma Hamisu Barau ya yaba ma kwazon mambobin karba da rarraba zakkar daidai wannan lokaci na bukatar.
Advertisement

labarai