Connect with us

KASASHEN WAJE

Ta’addanci: Rundunar hadin gwiwa ta kama mutum 202 A Kasashen Afirka

Published

on

Hadin gwiwar rudunonin tsaron kasashen Ghana, da Togo da Benin da kuma Burkina Faso sun yi nasarar kamo mutane 202 a kan iyakokin kasashen su daga ranar 15 zuwa 18 ga wannan watan da muke cikin sa., wadanda ake zargi da aikata laifuffuka daban daban.

Kanal Blaise Ouedrago shugaban rudunonin kasashen hudu dake aiki tare yace sun kama mutane 52 a Burkina Faso, 42 a Jamhuriyar Benin, 95 a Togo sai kuma 13 a Ghana.

Jami’in yace wasu daga cikin mutanen da aka kama na dauke da kayayyakin hada bama-bamai, wasu da bindigogi, banda haka sun yi nasara kama Babura 623 da ake amfani da su a kan iyakokin kasashen ba bisa ka’ida ba.

Hukumomin kasashen sun tabbatar da ci gaba da gudanar da irin wadanan ayyukan hadin gwiwa domin kawo karshen ayyukan ta’adanci daga mutane bata gari.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: