Muhammad Maitela" />

Ta’ammuli da miyagun Kwayoyi: YaKin baKi sai dubu ta taru

Jama’a masu biye da mu a wannan shafi, kamar kowane mako, a yau ma mun sake waiwayar batun ‘Ta’ammuli’ da miyagun Kwayoyi a tsakanin rukunan al’umma daban-daban, kuma al’amari ne wannan yake neman ya gagari kundila, wanda matuKar ba a dauki ingantattun matakai ba yana iya kasancewa babban Kalubale da zama tarnaKi a ci gaban zamantakewar yau da kullum; irin su tsaro, tattalin arziki da makamantan su.

Na yi tunanin sake tattauna batun ne, ganin irin yadda ya ke ci gaba da gudana kamar wutar daji, wanda a sannu a hankali yake ya gagari kundila, mtsala ce mai wuyar magani wadda a kebance daya ce daga cikin gagararrun matsalolin da suke nema su gunduri kowa, shawo kansa daidai yake da tunkarar fada da baKi; sai dubu ta taru!

A hannu guda kuma, idan mun yi la’akari da wannan babban Kalubale, al’amari ne wanda masana su ka tabbatar da cewa al’adar amfani da miyagun Kwayoyi, ya na da alaKa ta kusa da yaduwar aikata miyagun laifuka a Kasar nan da ma duniya baki daya. Sannan kuma, babban abin fargaba shi ne yadda yake mamayar sabbin jini, wanda a Karshe ya jawo musu fadawa tarkon badala da matsaloli kala-kala, tun a farkon rayuwar su, da bata makomar su; alhalin Kima da ci gaban kowace Kasa yana kan mizanin matasan ta.

A bangaren gwamnatoci, sun sha ayyana daukar Kwararan matakan yaKi da ta’asar sha tare da safarar miyagun Kwayoyin ta hanyar kafa hukumomi da kafa dokoki, wanda wani sa’in ba nan gizo ke saKar ba. Wanda Gwamnatin tarayya tana da hukumar NDLEA wadda aikin ta shi ne kai gwauro-mari wajen daKile yaduwar lamarin sha tare da safarar Kwayoyi masu sa maye a Kasar nan, amma lamarin ya ci tura, ganin har yanzu an kasa kaiwa ga manufar da aka samar dasu.

A halin da ake ciki yanzu, duniya ta na fuskantar babban Kalubalen mummunan sauyin da wadannan gagararrun matsaloli, wadanda ke neman canja alKiblar matafiyar al’ummar duniyar: shan miyagun Kwayoyi, safarar mutane, fama da cuta mai karya garkuwar jikin dan adam (HIB/AIDS), hadi da gurbatar yanayi.

Wanda shan Kwayoyi ba bisa Ka’ida ba da safarar su ke nema ya gagari kundila, sannan kuma barazanar da ke neman karya Kashin bayan ci gaban matasa a kowacce Kasa. Matsala ce babba, wadda har yanzu ba a gano lagon ta ba, musamman yadda abin ya fi Kamari ga matasa masu jini a jika; bangare muhimmi a ci gaba tare da kiyaye diyaucin kowacce Kasa a duniya.

Kuma kamar yadda masana suka bayyana, shan miyagun Kwayoyin wata mummunar al’ada ce wadda ta zama ruwan dare a tsakanin kowanne bangare na al’umma- maza da mata, yara da manya. Sannan ta’asa ce wadda ta shafi kowanne mataki na al’umma da mu’amalar yau da kullum. Lamarin da ya kaiwa kowa a wuya- saboda bayyanar sa a sarari tare da dandanar kudar sakamakon sa ga al’umma.

Har wa yau, shan miyagun Kwayoyi yana farawa ne daga lokacin da mutum ya yi amfani da magungunan da kamfuna (da makamantan su) ba a bisa Ka’idar da aka yi su ba, ko sharuddan da aka gindaya dangane dasu ba. Inda sau-tari yin amfani da irin wadannan magunguna ba bisa tsari ba, kan yi tasiri wajen sauya tunani da yanayin mutumin da ke shan su.

A wani bincike wanda cibiyar nazarin amfani da magunguna ba a bisa Ka’ida ba, kana da gano illolin da hakan ke haifar wa, ta ankarar da cewa tun a tashin farko ana iya gano yadda shan miyagun Kwayoyi zai yi illa ga rayuwar mutum- a rayuwar matasa, idan sun girma: musamman ga matasan da suka fara ta’ammuli da Kwayoyi a shekaru 14-tasirin miyagun Kwayoyin zai bayyana ne daga shekarun su na 21 zuwa abinda ya yi sama.

Wasu ginshiKan dalilan guda uku da ake kyautata zaton su ne dalilin tsunduma a ta’ammuli da miyagun Kwayoyi!

Binciken KwaKwaf wanda cibiyar ‘National Institute On Drugs’, ta gudanar, ya nuna yadda wadannan tadodi suka zama umull-haba’isar tsunduma a harkokin shan miyagun Kwayoyi, kamar haka:

  1. Abokantaka/samartaka: bincike ya gano cewa, abokantaka ko samartaka a tsakanin sabbin jini, yana da tasirin gaske wajen fadawar matasa tarkon shan miyagun Kwayoyi. Lamarin da bai tsaya kan matasa kadai ba, ya Kunshi kusan kowanne matakin rayuwa da yanayin da mutum ya tsinci kan sa tare da mutanen da yake mu’amala dasu.
  2. Halayyar kwaikwayo daga wasu: Da dama daga cikin wasu matasa, sun tsunduma a ta’ammuli da Kwayoyi ne ta hanyar yadda suka lura da wasu mutane a muhalli na zuKa ko kwankwadar kwaikwayon wasu abokanan su ke ta’amulli da Kwayoyin, ko tasirin zamantakewa a muhallin. Saboda yadda lokuta da dama, mutum kan yi aron dabi’u da al’adu, kamar yadda ya ga wasu nayi.
  3. Tsammanin samun nutsuwa: yayin da wasu matasa kan tsinci kai dumu-dumu, ya jefa su shan miyagun Kwayoyi ta dalilin halin damuwa, domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali

A tunanin da suke dashi, shan miyagun Kwayoyi ne kadai zai iya rage radadin damuwar da ke ci musu tuwo a Kwarya. Wanda kuma ba a nan gizo ke saKar ba, saboda shan miyagun Kwayoyin ba shi da alaKa wajen magance matsalar, wanda ta sakamakon hakan matsalar ta ribanyu. Wasu manazarta suna da ra’ayin cewa rashin aikin yi- shima yana taka rawa wajen tsundumar matasa yin ta’ammuli da miyagun Kwayoyi a Kasar nan.

Bugu da Kari kuma, akwai wasu manyan Kalubale guda biyu wadanda suke tattare da shan Kwayoyi masu sa maye; kaiwa ga zama alaKaKai ga lafiyar mutum da kuma yadda suke tasiri a canja tunanin mai mu’amala dasu.

Kana da yadda gwamnati ke taka rawa kai-tsaye ko a kaikaice wajen shigowa da su tsibi-tsibi ta halastattun Kwayoyi- kafin a jirkita su zuwa haramttun hanyoyi. Sannan wani zubin, da yadda gwamnati ke samun kudin shiga wajen shigo dasu, ta inda take tsula kudin harajin su- kamar irin su giya da taba sigari, baya ga lahanin da suke dashi ga lafiyar jama’a.

Baya ga illolin da shan giya da taba sigari ke haifarwa ga lafiyar jiki da KwaKwalwa, akwai Karin wasu miyagun Kwayoyi masu mummunar illa sosai, kuma wadanda ya kamata ace gwamnati ta dauki matakan hana shigo dasu- ayarin Kwayar ‘nаrсоtіс’. Wadannan sumfurin Kwayar zaKami ce masu lahani sosai, wadanda suke dauke da sinadarin ‘codeine’ da ‘hеrоіn’ da makamantan su.

Wanda a halin da ake ciki yanzu, ana iya cewa wadannan samfurin wadannan Kwayoyi da dangogin su, sun zama ruwan dare a Nijeriya, gasu nan zube birjik a shaguna da kan titi, ana sayarwa.

Wadannan nau’uka na miyagun Kwayoyin da jama’a ke hadiya dare da rana- safiya da marece, suna haufar da matsaloli daban-daban a lafiyar jiki da KwaKwalwa ga mai shan su. Kuma wannan yana zuwa ne idan an yi amfani da Kwayoyin ba bisa shawarar Kwararrun likitoci ba.

Dadin-dadawa kuma, masana sun ankarar da cewa, sakamakon da shan Kwayoyi ba bisa Ka’ida ba ke haifar wa sun Kunshi:

  1. Yana jawo yaduwar ayyukan tarzoma da tashin-tashina a cikin al’umma.
  2. Hambudar miyagun Kwayoyi yana kawo koma bayan tattalin arziki a cikin Kasa, ta yadda ake kashe kudi ba inda ya dace ba.
  3. Amfani da Kwayoyi barkatai, babbar barazana ce ga lafiyar al’umma- yanayin da ke haifar da bullar sabbin cutuka daban-daban tare da jawo yawaitar mace-mace a cikin gaggawa.

Bisa ga haka ne cibiyoyin binciken yanayin lafiyar al’umma tare da hadin gwiwa da masana halayyar dan Adam, suka yi yunKurin bai-daya wajen bayar da shawarwari dangane da yadda za a rage kaifin wannan annoba ta shan miyagun Kwayoyi.

Shi ne dole iyaye su dauki nauyin sa ido kan su waye abokanan ya’yan su, kana da yin tsayin daka wajen baiwa yaran su kyakkyawar tarbiyya da hana su aikata munanan dabi’u.

Har wa yau, ya kamata gwamnati ta dauki Kwararan matakan yaKi da shan miyagun Kwayoyi, ta hanyar amfani da makarantu wajen koyar da dalibai illolin shan miyagun Kwayoyi.

Sannan da daukar matakin yunKurin bai-daya, tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da Kananan hukumomi wajen fadakar da jama’a dangane da illolin amfani da Kwayoyi ba bisa Ka’ida ba.

Bai wa likitoci horo na musamman dangane da yadda za a bullowa lamarin Kwayoyi masu sa maye a cikin al’umma. Sannan kuma gwamnatoci su dauki halin ba sani ba sabo, wajen samar da ingantattun dokoki domin hukunta duk wanda aka samu da laifin sha ko safarar miyagun Kwayoyi.

Exit mobile version