Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tokacinmu na yau zai yi duba ne game da tsananin kishin da wasu matan ke da shi, ta yadda ke sawa su yi wa abokan zamansu illah ta kowacce hanya, wanda kuma hakan ya zama ruwan dare gama duniya a yanzu, musamman yadda Mata ke kona abokan zamansu da gangan. Duk da cewa ba dukka mata ne aka taru aka zama daya ba, amma hakan na ci gaba da yawaita tsakanin abokan zama a yanzu. Wannan ya sa shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; Ko mene ne riba ko alfanon yin mugun kishi da wasu matan ke yi? hakan na nuni da tsananin son da mace ke yi wa mijin ne ko wani salo ne nata na daban? Idan kai ne mijin wanne mataki za ka dauka? Ko laifin waye tsakanin mijin da matar, kuma me yake kaho hakan, ta wacce hanya za a magance afkuwar hakan?. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Musbahu Muhammad Goron Dutse Jihar Kano:
Abin da suke yi ba shida amfani kwata-kwata kuma jahilci ne da hauka. Ba shida wani amfani kuma ba soyayyar miji bace, saboda indai mace tana son mijinta to za ta so ‘ya’yansa ko da kuwa ba ta son uwar ‘ya’yan. Idan ni ne zan sallameta ne ta koma gidansu saboda babu riba a zaman Aure da irin wadannan matan, kuma za ta lalata zumunci tsakanin ‘ya’yan mutum ne. Laifin macen ne gaba daya domin shi kishi ba haka ake yinsa ba, ‘sometimes’ ma kishi ‘competition’ ne a tsakanin mata. A dinga hukunta duk macen da aka samu da laifin cin zarafin ‘ya’yan mijinta, ta haka ne za su daina aikata hakan. Mata su sani shi kishi abu ne me kyau amma a wajan kyautatawa maigida da kulawa da shi, amma mugun kishi hauka ne da kuma jahilci.
Sunana Fadila Lamido da ga Jihar Kaduna:
Ai irin wadannan matan abin tsoro ne, duk macen da za ta nufi kishiyarta da kisa ko akasin haka ba ta da Imani ne kowa ya nisanta kansa daga gareta, don kowa ma za ta iya nufarsa da hakan da zaran an bata mata ranta ba sai kishiya ba, don ni a nawa tunanin rashin imani ne ba kishi ba, irinsu ne idan wani abu ya hada ka da su kai ka ma manta sun yi ta bibiyarka, idan Allah ya basu dama su watsa maka wani abin da zai cutar da kai a rasa waye da aikin dan kai a tunaninka ba kada abokin gaba. Na san akwai mata masu mugun kishi amma duk abin da za su yi na rikici bai wuce ta fatar baki, wannan shi ne kishi, kuma shi ma idan yayi yawa abin yana zama kamar rashin sannin ciwon kai, don matar da ta san kanta ba za ta bari kishiya ta san me ke bata mata rai ba, mafi akasari kuma maza na taka muhimmiyar rawa wajen hura wutar rigima a tsakani ta hanyar kasa yi musu adalci, domin babu macen da za ta so ta ga an fifita daya komai hakurinta dole zuciya sai ta sosu. Sharawata ga mata masu mugun kishi su sassautawa rayuwa, su daina saka kishiya a gabansu su fuskanci abubuwan dake gabansu sai zuciya ta zauna lafiya, idan kuma ita ke shiga gonarki akwai hanyoyin da za ki bi cikin hikima da mutunta kanki a ja mata kunne, idan har mijin na da adalci kuma ya zama namiji a gidanshi zai fuskance ki ko da ace ke ce karama.
Sunana Ibrahim Ismail Ibrahim daga Jihar Kano:
Da farko dai hakan ba abu ne mai kyau ba, kuma mutum ba zai so ace ‘ya’yansa walau ko mace ko na miji su tashi da irin wannan dabi’ar mara kyau ba, dan burin kowa ‘ya’yansa su tashi da hali mai kyau. Hakan baya nuna so ne, duk wanda yake sonka ai ba zai cutar da kai ba, ko ya cutar da abin da kake so ba. Zan yi mata nasiha idan bata gyara ba zan rabu da ita. Toh! ba za ka iya cewa ga me laifin ba, tunda gaba daya ba a iya ganewa masu irin halin walau namijin ko mace kafin aurin, mataki shi ne mutane su dage da rokon Allah yayin da za su yi aure, Allah ya hada su da maza nagari, haka kai ma namiji idan zai ka yi aure kar ka ce iya kyau za ka bi, ka dage da rokon Allah ya baka mace ta gari, Allah ya ganar da mu.
Sunana Yakubu Producer Mai Company Gwammaja Entertainment Kannywood:
Rashin ilmin addini dana boko ne, shi kishi wani abu ne kamar halitta mace ko namiji kowa da kalar nasa, amma idan ya zo da yunkurin kisa ya zama jahilci da rashin tsoron Allah kenan, mikawa shaidar ragama ne kishinki sana’arki idan ba ki da jari ki rungumi nafiloli da azkar wato ammaton Allah. Idan na ci karo da me halin ba abin da zan yi face addu’a da rarrarshi idan abin ya damen na sallameta gaskiya. Hakuri da gaskiyar zamantakewa Shawark su daure zuciya su san kowacce mace da mijinki ya aure kowa rabonsa zai ci ba za ta ci naki ba, ke kanki sai kin cinye rabonki za ki koma ga Allah.
Sunana Zee Khair (Gwammaja Entertainment Kannywood):
Shi dai kishi dai Hausawa suka ce kumallon mata, amma indai har ta kai ga kisa ko halaka abokiyar zamanki ina ga za mu iya kiranshi da hauka. Ni ban ga wata riba a mugun kishi ba dan bata haifar da da mai ido, hakurin dai shi yafi tunda Allah ya hallice mu a musulmai ina tunanin ko wace mace ta san karin aure ba wani abu bane daya sabawa Addinin mu. A gaskiya ni dai a nawa ra’ayin miji mai mugun kishi ko mace mai mugun kishi ba abokan zama ba ce, saboda zai iya cutar da ni, idan bai kashe kansa ba to lallai zai kashe ni wataran.To an ce dai hallita ce kishi saboda haka ba za a iya kiranshi da laifin kowa ba, amma ta wani bangaren za a iya cewa laifin Oga ne idan baya yin daidai tsakanin iyalan sa, hakan ma na jawo kishi, dole sai ya gyara. Shawarar da zan bawa ‘yan uwa na mata shi ne indai Allah ya hadaki da abokiyar zama dole sai an yi hakuri da kau da kai, kuma mu ci gaba da Addu’ar Allah ya ba mu zaman lafiya mu da abokan zaman mu, ya kuma bawa mazajen mu ikon yin adalci a tsakanin mu.
Sunana Aliyu Isah Rano LGA, Zinyau G/Murabis (Gwammaja Entertainment):
Rashin tunani ne ita kishiya ai abokiyar zama ce. Wasu tananin kishi ne kawai ke janyo hakan. Idan na ci karo da me dabi’ar kokari zan yi na shiryasu, idan haka ba zayyu ba na raba mu gida. Lafin macen ne kuma hanyar gyaruwar hakan a nasiha da addu’a, ka mika lamarinka ga Allah. Su yi hakuri domin zaman duniya mai karewa ne duk kan abin da hakuri bai bayar ba, rashin shi ba zai bayar ba, duk wadda take da wannan halayyar Allah ka shirye ta.
Sunana Princess Fatimah Mazadu Gombe:
Da farko zan fara mika godiya ta ga Allahu subhanhu wataala, Allah ya karawa Annabi daraja. Hakiaa abun yana min ciwo sosai wallahi dan abu ne wanda ya dawo kamar ruwan dare. Abu ne marar amfani da zubda daraja, da kimar ki na ‘ya mace, baki halicci mutum ba ki ce za ki kashe shi? Wa’iyazu billahi, mata shi aure fa halal ne, dan ya kara aure sai ya zamana ta zamo abokiyar fada da gaba?, bai kamata ki biye wa zuciya ba wallahi a wurin. Ba shida riba sai zallar rashin hankali, ba shida amfani sai zallar sanya rigar rashin hankali, eh! toh wasu tsabar so ne, amma soyayya ai ba hauka bane, wasu kuma jahilci dan mazan ma akwai rawar kai in an ce za su yi aure dan wallahi duk hakurinki sai kin gaza. In n ci karo da me halin, hakuri zan tunasar da ita, sannan fada mata kuskuren aikata abin da take da niyyar yi, sannan na yi mata wa’azi na zamantakewa. Laifin maza ne, dan wasu suna da alkawari tsakaninsu da matan akan ba za su yi aure ba har abada, sannan wasu mazan in za su yi aure kamar mahaukata suke rikidewa su yi ta yi wa mace rashin mutunci, especially in akwai inda kika gaza masa kadan. Shawara Maza su rage rawar kai su ji tsoron Allah su sanya niyyar adalci a zuciyoyinsu. Shawara ta gaba In Allah ya riga ya jarabceki da auren namiji mai son aure ki danne zuciyar ki kiyi hakuri ita ma wacce za a karo wallahi kwanaki zuwa shekaru za ku dawo daya in kin yi hakuri. Mata a daure ayi hakuri duk da ni ma inada kishin, amma a zahirance ba zan yi wannan haukan ba, Allah ya kyauta.
Sunana Mustapha Aliyu daga Jihar Kaduna Birnin Gwari LGA (Gwammaja Entertainment):
Da farko akwai rashin ilimi na addini ga ‘ya mace, kuma har da laifin mijin da wata za ta yi wani abu da zai gani kuma ya je ba zai dauki mataki da wuri ba, domin ka faranta wa wata. Gaskiya babu wani alfano duk wanda za ka same su suna wannan zaman suna yi ne kamar arne da kafiri toh ina lafiya. Wata tana kishin tayi abu wanda za ta burge mijinta ita ma dayar tayi, wata kuma idan ta ga dayar tana kokarin cutar musu da mijin za a ga tana bakin kokarinta ta ga ta kare shi daga sharrinta, wata kuma idan ka tambayeta akan me kike kishi da ita za a ji tayi shiru wato hakanan kawai. Idan na ci karo da me irin halin da farko zan yi yadda iddinin musulunci ya tanada, zan tara su in yi musu nasiha. Idan sun ki ji zan kira manya duk wanda taki jin magana tana nuni da bata yarda da abun da musulunci ya fada ba, sai ka san matakin da za ka dauka akanta. Da farko laifin mijin ne saboda kila sanda yake zuwa zance wajan dayar yana maganganun batanci akan dayar, ka ga idan ta shigo tana kallon dayar da abun da kake fada mata, kuma baka fito fili ka gaya mata gaskiyar abun da kake da shi ba. Laifin na maza ne kuma abun kafin kayi aure za ka gyara ba wai sai kayi aure ba. Shawara kawai dai su bi abun da musulunci ya fada shi ne kawai su yi hakuri.
Sunana Buhari Abdullahi daga Jihar Kano Unguwa Uku Layin Famfan Dan Yobe:
To maganar gaskiya abin da yake saka mata tsananin kishi abu daya ne; idan mace tana tsananin son mutum, tana Sonsa 100% to ko kuda ba ta so ya sauka a kansa. Idan ni ne mijin kawai zan ci gaba da fahimtar da ita mugun kishi ba abu ne mai kyau ba ta ringa kwantar da hankalinta. Shi kishi a zuciyar kowa yake baya zama a iya wani bangare. Abin da yake janyo kishi abu daya ne tsananin Soyayya, abin da zai magance afkuwar hakan gaskiya babu muddin akwai Soyayya. Ni dai shawarata ga matan da suke da mugun kishi shi ne su ringa kwantar da hankalinsu, kishi ya daina sa su yin wani abu da zai zamar musu dana sani.