Jama’a, me za ku ce idan kun ji an ce “tafarnuwa za ta iya haifar da barazana ga tsaron kasa”? Tabbas za ku dauki zancen a matsayin abin dariya.
Sai dai an ji zancen ne a bakin wani babban jami’in kasar Amurka. Dan majalisar dattawan Amurka, Rick Scott a baya-bayan nan ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa, tafarnuwa da aka yi nomanta a kasar Sin tana da “babbar barazana” ga tsaron kasar Amurka a fannin samun abinci mai inganci, ya kuma yi kira da a kaddamar da bincike bisa aya ta 301 ta dokar ciniki ta shekarar 1974 ta kasar Amurka. Kana majalisar wakilan Amurka ta yi nazari tare da zartas da “dokar ba da izinin tsaron kasa ta sabuwar shekarar kasafin kudi ta shekarar 2025”, wadda kuma ta hada da tanade-tanade da ke bukatar shagunan sojin Amurka hana sayar da tafarnuwar kasar Sin.
- Me Ke Kawo Zargi Tsakanin Wadanda Suke Gab Da Su Yi Aure?
- Saboda Isar Da Sako Nake Yin Shirin Manyan Mata Ba Domin Kudin Da Zan Samu Ba -Abdul Amart
Tafarnuwa ba ta taba tunanin za ta iya yin babbar barazana ga Amurka ba. Amma ba a rasa jin irin wadannan abubuwa cikin ‘yan shekarun baya bayan nan. Daga shigowa da motoci, da jirgi marasa matuki, da na’urorin daga kaya, kai har zuwa tafarnuwa, tamkar dukkansu na iya “haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka”. Amurka ta kusan haukacewa domin “tsoron kasar Sin”.
Sai dai al’ummar duniya suna gano cewa, Amurka na fakewa ne da batun “tsaron kasa” wajen daukar matakan kariyar ciniki, kuma tana neman dakile bunkasuwar kasar Sin. In mun dauki misali da tafarnuwa wadda ke ba Mr. Scott tsoro, kasar Sin na daga cikin kasashen da suke yawan samar da tafarnuwa, da kuma fitar da su zuwa ketare, ita kuma kasa ce da ta fi yawan fitar da tafarnuwa ga kasar Amurka, a cikin gomman shekaru da suka wuce, sau da dama kasar Amurka ta kara haraji a kan tafarnuwa da take shigowa daga kasar Sin bisa dalili na wai “kin yarda da sayar da kayayyaki da yawa da farashi mai matukar rahusa”, kuma Mr.Scott na daga cikin wadanda ke sa kaimin daukar matakin.
A wasakun da ya aikawa jami’an gwamnatin kasar Amurka, Mr. Scott ya ce wai “kasar Sin ta shuka tafarnuwa da gurbataccen ruwa”, yana mai bayyana damuwarsa game da yadda ake yawan shigowa da tafarnuwa daga kasar Sin. Amma a hakika, kasar Sin na da tsari mai tsanani da ake bi wajen gudanar da ayyukan gona, ciki har da noman tafarnuwa, idan da gaske ne tafarnuwar da ta samar na da matsala, to, hukumomin kwastan na kasar Amurka da ke kula da ayyukan duba ingancin kayayyakin da ake shigowa da su za su gano su, sam ba za a yarda da shigowar tafarnuwar kofar gidan Amurka ba.
Sanin kowa ne, Amurka ta sha yin kiran “’yancin takara”, da “’yancin ciniki” a yayin da take zargin wasu kasashe da rashin ’yanci a kasuwanninsu. Amma yayin da kasashe masu tasowa ke dada bunkasa, tare da cimma nasarori wajen kirkire-kirkiren fasahohi, Amurka ita kanta kuma masana’antunta na raguwa, nan da nan sai Amurka ta manta da ‘yancin ciniki da na takara, kuma ta dauki matakai iri iri na dakile abokan takararta, da ci gaban sauran kasashe.
Sai dai a zamanin da muke ciki na dunkulewar tattalin arzikin duniya, sassan kasa da kasa sun kasance suna cude-ni-in-cude-ka. Duk wata nasarar kirkire-kirkire ta kan samu ne bisa hadin gwiwar sassan duniya daban daban. Fakewa da batun tsaron kasa don siyasantar da harkokin tattalin arziki, da ciniki, da kimiyya da fasaha, ba zai haifar da komai ba, illa ya lalata tsarin samar da kayayyaki na duniya, har ma ya lahanta moriyar kai.
Shawara ga kasar Amurka ita ce ta mai da hankali a kan gano bakin zaren warware matsalolin da take fuskanta, kuma ta kalli ci gaban sauran kasashe yadda ya kamata, tare da rungumar hadin gwiwar kasa da kasa, hakan zai kawar da damuwarta game da kasar Sin, da ba ta damar gano hanyar kara raya kanta. (Mai Zane:Mustapha Bulama)