Rabiu Ali Indabawa" />

Tafkin Kongo: Shugabannin Afirka Sun Yi Taro

Shugabannin kasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka na ganawa a babban birnin Jamhuriyar Congo, Brazzabille, domin duba hanyoyin kare tafkin Congo, mai albarkatun daji da ruwa da dabbobi.

Bayan shugabannin na wadannan yankuna na Afirka, shi ma Sarki Mohammed na shida, na Moroko, wanda ya taimaka wajen kafa asusun samar da kudin kare tafkin, wanda ke fuskantar barazanar bannata daji shi ma yana halartar taron.

Wasu na kiran wannan tafki mai matukar muhimmanci da tarihi a matsayin huhun duniya na biyu, wato matattarar sarrafa iska, saboda bayan shi, katafaren surkukin dajin yankin Amazon ne kadai ya fi na Congon girman daji mai dausayi.

Shugabannin kasashen da suke ganawa a birnin na Brazzabille suna kokarin lalubo hanyoyin da za su taimaka wa jama’ar yankin su ci gaba da rayuwa yadda ya kamata ba tare da suna yi wa daji da kogunan na Congo illa ba.

Haka kuma a lokacin taron nasu za su tattauna kan daya daga cikin manyan ayyuka da ke cike da buri, wanda shi ne na, yadda za a karkatar da ruwa daga cibiyoyin da ke ba wa Kogin na Congo ruwa zuwa tafkin Chadi wanda ke fuskantar barazanar kafewa.

Bayan haka shugabannin za kuma su duba batun wata babbar barazanar da ke addabar dajin na Congo, wato aikin sare bishiyoyi domin samar da katako.

A kwanan nan aka soki lamirin gwamnatin Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo saboda ba da dama da ta yi ga wasu kamfanonin kasar China na sare bishiyoyin katako a fadin murabba’in kilomita dubu shida a dajin na Congo.

Kungiyoyin kare muhalli sun ce wannan yarjejeniya da gwamnatin kasar ta Congo ta yi da kamfanonin na China ta saba dokar da kasar ta yi a shekarar 2002 kan ayyukan kamfanoni na sare dazuka.

Exit mobile version