Connect with us

LABARAI

Taimakon Allah Ne Jigon Samun Zaman Lafiya A Masarautar Bauchi —-Sarkin Bauchi

Published

on

Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji (Dakta) Rilwanu Sulaiman Adamu, ya bayyana asalin sirrin dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake samu a karkashin Masarautarsa tun lokacin da ya dale karagar mulkin fadar har zuwa yau.
Sarkin ya shaida cewar ikon Allah ne kawai da sallama masa tare da komawa gareshi a kowani lokaci su ne sirrin daurewar zaman lafiyar da ake samu, yana kuma cewa sirrin na gaba shine sauraron kowa da baiwa kowa hakkinsa tare da amsar shawara ga duk wanda ya kawo masa.
Dakta Rilwanu ya shaida hakan ne a lokacin da ke ganawa da wakilin LEADERSHIP A YAU ASABAR da ke Bauchi jiya dangane da cikarsa shekaru 10 cif a bisa karagar mulkin Masarautar, wanda ya ke mai nuna dumbin godiya ga Allah a bisa amince masa ya kawo wannan lokacin cikin kwanciyar hankali da koshin lafiya tare da samun girmamawa da fahimtar juna daga al’umman masarautarsa.
Alhaji Rilwanu dai shine sarkin Bauchi na 11, ya cika shekaru goma a kan mulki ne a jiya Alhamis 30 ga watan Yulin 2020, wanda aka gudanar da addu’o’i na musamman a matsayin gagarumin bikin raya wannan shekarun wanda ya samu halartar sassa daban-daban da suke jihar.
Wakilinmu ya labarto cewar jihar Bauchi tana daga cikin jihohin da suke shiyyar arewa maso gabas duk da fama da aka yi ta yi da matsalar tsaro da fama da ‘yan Boko Haram Allah ya taimaki jihar ba ta fuskaci matsalolin sosai ba dukka kuwa a karkashin Sarkin aka samu wannan nasarar domin ya amshi ragamar masarautar a shekarar 2010.
A cewar Sarkin na Bauchi; “Ikon Allah ne, ba mu da wani hanzari ko dabara sai ta Allah. Wai Bahaushe ya ce idan ka ga gemun dan uwanka ya kama da wuta ka shafa wa na ka ruwa. Mun ga irin abubuwan da suka yi ta faruwa sai muka ga ba mu da wata dabarar da ta wuce mu koma ga Allah; Allah Ubangiji shine madogara, nan take muka dogara muka koma ga Allah ga kuma abun da Allah ya mana.
“Bayan haka, sai Allah ya taimakemu muka hada kai da kafa. Shi harkar tsaro kowa da ka ganshi ya shafeshi, har kai kanka da nake magana da kai kana da irin rawar da za ka taka. To sai muka bada dama wa kowa ga musulmi da kirista babba da yaro mace da na miji kowa muka ba shi dama duk mai shawara a kowani lokaci ya zo ya kawo za mu saurari mutum. Mu shawara komai kashinsa ba mu wasa da shi musamman abun da ya shafi tsaro.
“Cikin ikon Allah muna zaune a nan wane zai zo ya ce mana mai martaba ga kazan nan ga abun da za a yi mu ce mun gode, wani ya zo ya ce ga abun da za a yi shi ma mu ce mun gode, to ka ga hakan da dadi, kamar dai yanda na fada maka Allah shine madogararmu. Muna fatan sauran wurare za su koyi da wannan abun domin daurewar zaman lafiya a cikin kasarmu,” Inji Mai martaba Sarkin Bauchi.
Sarkin mai shekaru 50 a duniya ya kuma gode wa Allah ta’ala da ya nufa ya ga wannan babban rana a gareshi, tare da addu’ar Allah ba shi karsashin ci gaba da rike jagorancin da ke kansa.  A daya barin, ya gode wa irin gudunmawa da hadin kai da gwamnatin jihar ke ba su wajen tabbatar da kyakkyawar jagoranci, “Sauraron Shawarorinmu da goyon baya da gwamnati ke ba mu abun mu gode mu yaba ne bisa jin dadin hakan da muke ji bisa amsar shawararmu mai dadi ko marar dadi.
“Muna godiya wa dukkanin jama’an jihar Bauchi a iya wannan shekarar da Allah ya kawo mu tabbas al’umma sun kaunacemu, sun mutuntamu, sun martaba mu, babu abun da za mu ce garesu sai godiya da fatan Allah ya saka wa kowa da alkairi.
Muna kuma sake godiya da fatan alkairi ga dukkanin jama’an da suke wannan jihar da niyyar duk wanda yake sana’a ko ta hannu da sauran nau’o’in sana’a Allah ya kara albarka wa abun da ake yi. Ma’aikata da ‘yan kasuwa Allah kara bunkasa tattalin arzikinmu, ‘yan makarantanmu muna muku fatan alkairi, matasanmu a kullum muna addu’ar Allah ba su abun dogaro da kai.”
Advertisement

labarai