Cikin jerin bayanai daga ‘yan jaridar Afirka, ‘yar Ghana Elizabeth Ohene ta yi rubutu game da irin rikicin da ake yi kafin binne shugabannin Afirka.
“Ba ni da tabbas ko zan iya ba da wani taKadirin zance, amma ni ban taba sanin cewa kasancewar mutum shugaban wata Kasa a Afirka zai iya haddasa rigima a Kabarinsa ba idan ya rasu.
Na yi ta bin rikicin da ake yi game da inda za a binne Tsohon Shugaban Kasar Angola José Eduardo dos Santos, wanda ya rasu a Sifaniya ranar 8 ga watan Yuli.
Shugaban Kasar mai-ci João Lourenço da kuma matar Dos Santos na son a mayar da gawarsa gida don yi mata jana’izar ban-girma a Kasaitacciyar maKabarta ta musamman – abin da muke gani na girmamawa ga shugabanni a Ghana.
Amma ‘yarsa mai suna Welwitschia “Tchizé” na son a yi masa jana’iza a killace kuma a binne shi a wani Kabari na musamman a Sifaniya ta yadda ‘ya’yansa za su iya ziyartarsa,” in ji ta.
Ta ce wasu daga cikin ‘yan uwanta na goyon bayan Kudirin nata, wadanda ke fuskantar zargin cin hanci kuma za a iya kama su da zarar sun saka Kafa a Angola.
Daya daga cikin ‘ya’yan Dos Santos ya ce ba Kasar ce ke da alhakin daukar nauyin jana’izarsa ba kuma iyalinsa ne ya kamata su yanke hukunci.
Maganar cewa ko Kasa na da iko kan gawar shugabanta ba sabon abu ba ne.
An samu irin wannan lamari a Zimbabwe a 2019, lokacin da Robert Mugabe ya rasu shekara kusan biyu da suka wuce bayan ya shekara 37 a kan mulki – inda shugaba mai-ci Emmerson Mnangagwa ya kawo Karshen mulkin nasa tare da goyon bayan sojoji.
Kowa ya yi tunanin za a binne shi ne a Filin Gwaraza na Kasa ( Heroes’ Acre) da ke Birnin Harare.
Ko ma dai mene ne, shi ne ya gina Heroes’ Acre kuma ya binne da yawa daga cikin abokan gwagwarmayarsa, ciki har da Sally matarsa ta farko.
Mista Mnangagwa ya fara gina Kabari na musamman don binne jagoran neman ‘yancin, amma kuma iyalansa ba su amince da hakan ba ganin yadda aka kore shi daga mulki kuma abokan gwagwarmyarsa suka yaudare shi.
Bayan shafe makonni ana taKaddama, iyalinsa sun yi nasara kuma an binne Mista Mugabe, jagora kuma gwarzo a Zimbabwe, a Kauyensu ba tare da wani wakilin gwamnati ba.
Hatta Kenneth Kaunda – shugaban Kasa na farko bayan ‘yancin kai a Kasar Zambia kuma daya daga cikin ‘yan gwagwarmayar neman ‘yanci – bai iya samun wurin da za a binne shi ba ba tare da rikici ba.
A cewar iyalinsa, ya so a binne shi kusa da matarsa ba inda gwamnati ta tanada ba.
Zuwa yanzu dai iyalin nasa ba su yi wata jayayya ba yayin da “KK” – kamar yadda ake kiran sa da shi – na ci gaba da kwanciya a Embassy Memorial Park da ke Lusaka baban birnin Kasar.
Daga gudun hijira zuwa girmamawa
“Wadannan rikice-rikice kan gawarwaki ba sabbin abubuwa ba ne. A nan Ghana, mun saba da irin wannan.
Shugaban Kasarmu na farko Kwame Nkrumah ya rasu a Bucharest na Romania lokacin da yake jinya.
Da farko an binne shi a Conakry, Guinea bayan ya shafe lokaci yana gudun hijira a can. Daga baya aka mayar da gawarsa Ghana. An yi masa jana’izar gwamnati a Accra sannan aka binne shi a Kauyensu na Nkroful.
A lokuta daban-daban za ka dinga jin iyalansa na cewa a dawo musu da gawarsa.
A 2012, shugaban Kasarmu John Atta-Mills ya rasu yana kan mulki amma samun wurin da za a binne shi ya zama aiki.
Wasu daga cikin iyalansa sun nemi a kai gawarsa Kauyensu, sai dai ba su samu wani goyon baya ba a lokacin.
An Kyale wurin da gwamnati ta haKa a matsayin Kabarinsa saboda bai dace da shi ba. Daga baya aka mayar da shi wani wuri daban.
An tsara cewa wurin shaKatawar da aka binne shi ya zama maKabartar shugabannin Kasa.
Tun daga wannan lokaci, wani shugaban Kasar – Jerry Rwlings – yara su.
Ba kai shi wurin da aka binne Shugaba Atta-Mills kawai ba, iyalansa sun zargi gwamnati da aiwatar da hakan ba tare da izininsa ba.
An binne shi a maKabartar sojoji da ke Accra tare da yi masa jana’izar girmamawa.
‘Yan makonni da suka wuce muka yi bikin cika shekara 10 da mutuwar Atta-Mills.
Har yanzu ana cecekuce a kan kushewarsa: wane ne zai kula da ita kuma me za a rubuta a kanta.
Akwai kuma wasu daga iyalansa da ke son a tono gawarsa daga inda gwamnati ta binne shi a Accra zuwa Kuyensu don a sake binne shi.
Saboda haka ina ganin daya daga cikin matsalolin zama shugaban Kasa a Afirka ita ce ba lallai a samu wurin da za a binne mutum ba idan ya rasu,” a cewar ‘yar jaridar.