A halin yanzu yawancin al’ummun da ke zaune a garuruwan iyakokin kasashen Nijeriya da Nijar sun shiga tsaka mai wuya sakamakon zaman zullumi a kan yiyuwar yaki a tsakanihn Nijar da kungiyar ECOWAS, tun bayan karewar wa’adin da kungiyar ta ba shugabannin sojojin da suka yi juyin Mulki, na su mayar da tsohon shugaban kasar da suka hambare, Mohammed Bazoum a kan karagar mulki ba tare da bata lokaci ba.
Tuni dai al’ummun yankunan iyakokin suka fara dandana radadin takunkumin tattalin arzikin da kungiyar ECOWAS ta kakaba wa sojojin da suka yi juyin mulkin.
Zirga-zirga a tsakanin al’ummun da ke zaune a iyakokin ya fara neman tsaya cak, harkokkin kasuwanci da na tattalin arziki shi ne ya fi fuskantar matsala a halin yanzu. Wakilanmu sun bayyana cewa, mutane na zama cikin tsoron rashin sanin mai faru a nan gaba.
Al’ummun da ke zaune a yankin iyaka na Jibia-Magama da ke Jihar Katsina sun nuna rashin jindadinsu a kan shawarar kungiyar ECOWAS na mamaye Nijar in har sojoji basu dawo da Bazoum kan mulki ba.
A cewarsu, kulle iyakoki da aka yi, ya durkusar da harkokin tattalin arziki a yankin hakan kuma ya haifar da rashin aikin yi a tsakanin matasa wanda kuma hakan ya jefa wasu daga cikin su barace-barace a kan tituna, a mastayin haya data tilo da za su samu abin ciyar da kansu.
Tabbas shawarar ECOWAS ya matukar shafar rayuwar al’ummar iyaka na Jibia-Magama musamman ganin suna zaman zullumin rashin sanin abin da zai faru a nan gaba.
LEADERSHIP Hausa ta gano cewa, tuni aka garkame iyakar Jibia-Magama, babu zirga-zirgan motoci a tsakanin iyakokin, sai dai an lura wasu manyan motoci an faka su a gefen hanya suna jiran tsammani.
Wakilanmu da suka ziyarci yankin sun lura da yadda wasu mutane ke takawa da kafa suna shiga bangaren kasa Nijar don cin wata kasuwa a garin Dan Isah.
haka kuma wasu ‘yan kasuwa da suka samarwa kansu hanyoyin shiga kasuwannin yankuna suna harkokin kasuwancinsu don samarwar kansu mafita sakamakon matsalolin da kulle iyakar da kuma cire tallafin man fetur ya haifar.
Haka kuma jami’an tsaron sun kafa shingen bincike a wasu haramtattun hanyoyin da ake amfani da su don shiga da fitar da kayayyaki, amma duk da haka mutanen suna nemawa kansu hanyoyin tafi da rayuwar su don ba zai yiwu su jure wannan hali na matsi da suke fuskanta ba.
Wani mazaunin yankin, mai suna, Alhaji Abubakar Magama, ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa cewa, basu ji dadin shawarar kulle iyakoki ba, don kuwa ya haifar wa da matasan yankin rashin aikin yi wanda kuma hakan ya haifar da gaba a tsakanin al’ummun yankunan Nijar da na Nijeriya.
Ya kara da cewa, “Bamu san da wani tallafin man fetur ba kafin wannan lokacin, mun dai san a kwai kayayyaki masu arha a Nijeriya, amma abin ba haka yake ba a yanzu. Babu wani dan Nijeriya da zai buga kirji ya ce yana cin abinci sau uku a rana ko kuma ya ce yana iya ciyar da bako, saboda tsananin halin da ake ciki.
“A halin yanzu safarar kayayyakin abinci daga Jibia zuwa garin Katsina sai mun kashe kudade masu yawa saboda yawan shingen binciken jami’am tsaro da aka sanya a kan hanya, yanzu kuma kulle iyakar da aka yi ya kara haifar da karin matsaloli gare mu. Muna son gwamnati ta sanar da mu shin a wani bangare muke? Nijar ne ko Nijeriya?”
Haka kuma wani mai suna Musa Shehu, wanda ke kwance a cikin wata babbar mota a kan iyakar Jibia-Magama, ya ce yana nan fiye da mako daya, tun da aka sanar da kulle iyakar.
Ya ce, yawancin motocin da suka makale suna a kan hanyarsu ne ta zuwa Kano, Kaduna, Legas ko kuma Abuja amma aka hana su shigowa Nijeriya saboda wannan matsalar.
Shehu ya kara da cewa, kudaden abincinsa sun kusa karewa, ya nemi gwamnati ta gagguta bude iyakokin don harkokin kasuwanci da walwalar jama’a su ci gaba ba tare da bata lokaci ba.
Wakilanmu da suka tattauna da al’ummar da ke zaune a garuruwan Dolekaina, Tungar Sule da Kamba a bangaren Nijeriya da kuma al’ummun Tungar Gyado da Peka da ke bangaren jumhoriyyar Nijar sun nuna bacin ransu a kan barazanar kungiyar ECOWAS na mamaye Nijar tare da shirin kai hari a kasar.
A cewarsu, tun da sojoji suka hambarar da gwamnatin kasar Nijar al’ummun da ke zaune a yankunan iyaka na Nijeriya da Nijar suke fuskantar kuncin rayuwa.
Sun ce, harkokin rayuwar ya kara tabarbarewa ne sakamakon katse wutar lantarki, tsadar kayan masarufi da man fetur da ake fuskanta a yankunan.
A tattaunawarsa da Wakilinmu a garin Dole Kaina (bangaren Nijeriya) Sarkin kauyen mai suna Alhaji Sani Dolekaina, ya bayyana cewa, bangaren Dole Kaina na Nijeriya da Dole Kaina na bangaren Faransa basu ji dadin wannan lamarin ba gaba daya.
Ya ce, kafin juyin mulkin, bangarorin al’ummun biyu na zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsu, suna auratayya a tsakaninsu, suna gudanar da harkokin al’adun gargajiya a tsakaninsu ba tare da wata matsala ba, tare da sauran harkokin yau da kullum a tsakaninsu.
Ya ce, abin da suke bukata a yanzu shi ne zaman lafiya wadda za a iya samu ta hanyar tattauna da fahimtar juna a tsakanin kungiyar ECOWAS da sojoji masu juyin mulki.
Haka kuma Sarkin kauyen Dolekaina na bangaren Faransa, Alhaji Mohmud Yousofu, ya ce, duk da cewa, babu wani abin da ya canza a bangaren zamantakewa a tsakaninsu da al’ummar Nijeriya amma a yanzu babbar matsalar su shi ne tsadar farashin kayayyakin abinci.
Yawancin al’ummar da ke zaune a yankin iyaka na karamar Maigatari da ke Jihar Jigawa sun bayyana cewa, takunkumin da aka kakaba wa kasar Nijar tamkar an sanya wa dukkan al’ummar yankin ne gaba daya, don suna da zuriyya na kaka da kakanni a bangaren Nijar kuma hakan ya tsayar da harkokin kawusanci da zumunci a tsakaninsu.
Iyakar da aka tsaga a tsakanin Nijar da Nijeriya ba shi da wani tasiri don kuwa al’ummun biyu suna amfani abubuwa daya, kamar filin gonaki, kasuwanni, al’adu, yare da addini har ma da makarbarta a tsakanin su da mutanen Nijar da Nijeriya.
A ta bakin shugaban kasuwar Maigatari kuma daya daga cikin manya-manyan kasuwannin shanu a Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Ibrahim, ya ce, harkokin kasuwanci ya tsaya cak tun da aka fara wannan rikicin.
“Bamu yi maraba da juyin mulikin ba, ba kuma yi maraba da takunkumin da aka sanya ba, ‘yankasuwa da talakawa sune za su sha wahala daga dukkan wannan matakan da aka sa.”.
Sakataren kungiyar masu sayar da shanu na kasuwar, Alhaji Muhammad Duwa, ya ce, janye tallafin man fetur ya matukar shafar harkokin kasuwancinsu, haka kuma juyin mulki da kuma takunkumin da aka sa ya tsayar da harkokin kasuwar gaba daya.
“A yau al’amura ba kamar yadda suke a da ba ne, an shiga tsakaninmu da abokan huldar mu na kasuwanci, mutanen Nijar na shigo da dabbobi kasuwanninmu su kuma su sayi kayan abinci da wasu kayan masarufi, amma wannan takunkumin ya katse dukkan wannan abubuwan, muna cikin tsaka- mai-wuya”.
Wani mai suna Sale Ado, wanda direba ne da ya yi fiye da shekara 20 yana zirga-zirga da mota a tsakanin Nijar da Nijeriya ya ce, matsalar juyin mulkin ya jefa harkokin tattalin arzikin yankin cikin tsaka-kai-wuya, ya kara da cewa, rufe iyakokin Nijar da Nijeriya ya tsayar da harkokin zirga-zirgar motoci a tsakanin kasashen an kuma shiga cikin halin rashin tabbas a sakamakon haka a bangaren tattalin arziki da zamantakewa.
Haka kuma wani mai tuka babbar mota mai suna, Ali Dan’uku, ya ce, shi da yaransa 4 sun dogara ne da motarsa wajen gudanar da harkokin rayuwarsu, amma wannan takunkumin da aka sanya wa kasar Nija ya haifar musu da zaman janwgam yanzu basu da wani aiki a hannun su.
“A tsawon rayuwana na taba ziyartar jihar Kaduna da Kano ne kawai a Nijeriya amma babu inda ban taba shiga ba a kasar Nijar ta hanyar zirga-zirga da kayayyaki, mu a yankunan iyakokin Nijar da Nijeriya mun fi karkata wajen harkokkin kasuwancinmu zuwa kasar Nijar.”
In har shugabannin ECOWAS suka ci gaba da kokarin amfani da karfin soja wajen kawar da masu juyin Mulki a Nijar, al’ummun da ke a kan iyakokin kasar za su ci gaba da dandana kudarsu, wanda zai iya kaiwa ga haifar da miliyoyin ‘yan gudun hijira a tsakanin kasashen.
Wasu mata a kauyen Jobe masu suna Amina Ali, Fatima Musa da Raliyat Musa Sa’id, sun bayyana cewa, a halin yanzu sun tilastawa kansu shiga daji don neman abinci, sun ce takunkumin da aka sawa Nijar ya tsayar da harkokin kasuwanci a yankunan wanda ya haifar da rashin aikin yi ga yaransu.
“Rikicin ya matukar shafarmu sosai, yanzu gashi karfe 12 amma babu wanda ya karya saboda bamu da abincin da za mu ci. Saboda haka muna kira da a sausauta rufe iyakokin da aka yi cikin gaggawa a kuma warware matsalar da aka shiga tun kafin lamarin ya tabarbare,” in ji matan.
A cewar mataimakiin shugaban kungiyar masu manyan motoci masu aiki a tsakanin Nijeriya da Nijar da ke karamar hukumar Maigatari, ya bayyana cewa, halin da ake ciki a garuruwan da ke a iyakokin tsakanin Nijeriya da Nijar ya munana yana kuma shafar dukkan al’ummar bangarorin biyu ne gaba daya.
“Harkokin ayyukanmu na cikin garari, ni kaina ina da manyan motoci 15 a karkashina amma a halin yanzu duk mun ajiye su, don an kulle hanya, duk mun rasa ayyukanmmu, ba mu sana’ar da zamu yi a halin yanzu,” in ji shi.
Malam Shehu Isa na garin Adare da ke kasar Nijar ya makale a Nijeriya a cikin rikicin, ya bayyana cewa, ya ziyarci danuwansa ne a garin Ladan (wani kauye a karamar hukumar Maigatari), yanzu yana son komawa wajen iyalansa a kasar Nijar amma babu hanya duk an rufe. Ya ce lamarin ya fi tsananin da suka fuskanta a lokacin kullen annobar cutar korona.
Kafin wannan lokacin, garin Illela, gari ne da ake harkokin kasuwanci da na zamantakewa, basu da wata matsala kamar dai yadda yawancin garuruwan da ke a kan iyaka suke, ana kuma gudanar da harkokin sumoga a yankin, garin ya kuma kasance hanya ga masu gudun hijira zuwa tura inda suke bi ta Arewa ta Arewa, garin kuma ya kasance babbar kasuwar kasa da kasa na Illela, ‘Illela International Cattle Market’ inda ‘yan kasuwa daga kasashen Chad, Mali da Nijeriya suke haduwa suna gudanar da harkokin kasuwancinsu ba tare da wata matsala ba.
Akwai harkokin kasuwanci biyu a yankin iyakokin kasar nan, wadanda suke shirye su bi dokokin gwamnati da kuma masu shirin karya ka’ida da yi wa harkokin gwamnati zagon kasa.
Yanzu da aka kakaba takunkumin zirga-zirga a hanyar Illela zuwa Kwanni, masu motoci ‘yan kasuwa masu gudanar da harkokin kasuwanin yankin ne suke a kan gaba wajen dandana radadin takunkumin da aka sa.
Lamarin masu fasa kwauri kwua ya shiga mummunan garari don rufe iyakoki da aka yi tsayar da harkokinsu gaba daya.
Wani mai suna Salmanu Abdullahi, a garin Illela wanda ya tabbatar da cewa, shi bai san wata sana’a ba da ta wuce sumogulan kayayyaki, ya ce, tuni da aka rufe iyakoki, harkokin zirga-zirga da na kasuwanci ya tsaya cak basu sana bin da za su yi ba.
Ya ce, “Rufe iyakokin ya tsayar da dukkan harkokin kasuwanci a wannan garin, lamarin masu fasakwauri kuma ya kara zama mummuna tashin hankali.
Haramta sayar da man fetur a garuruwan iyakokin kasar nan da kuma cire tallafin mai da aka yi duk sun kara haifar da matsalar ga masu harkokin fasa kwauri a yankin iyakokin kasa.
A halin yanzu al’ummar yankin sai sun tafi har zuwa garin Gwadabawa don samun man fetur da za su yi amfani da shi.
Kafin rufe iyakokin suna aikin kwasan buhunna shinkafa daga garin Kwanni ta kasar Nijar, ko kuma su kashi matafiya wadanda basu da cikakken takardar fasfot na ECOWAS daga Illela zuwa garuruwan Gidan Kamin, Bakin Dutse, Geti, Babadede, Gidan Ketsu da kuma garin Tabanni.
Nura Usman, wanda shi ne ya zagaya da wakilinmu don ganin yadda lamarin ya ke tafiya, ya tabbatar da ikirarin Salmanu Abdullahi
Ya kuma kara da cewa, “Saboda kusuwacinmu da kasar Nijar, duk abin da ya shafe su ya shafe mu. Shawarar kulle iyakar mu da kasar Nijar a garin Illela kamar yadda gwamnatin data gabata ta yi a shekarar 2019, na tsawon shekara 2 ya fara shafar harkokin rayuwarmu.
Fiye da motocin kamfanin siminti na Dangote 100 suka makale a bangaren Nijar sakamakon wannan dambarwar.
Wani mai suna Aminu Illela, dan shekara 38 mai ‘ya’ya 6 wanda yake sana’ar kankara ya bayyana yadda ya shiga matsala sakamakon rufe iyakar da aka yi musamman ganin yadda harkokin kasuwanci ya tsaya cak a yankin.
Rufe iyalar lllela ba labari ne mai dadi ga ‘ya kasuwan ‘Illela international cattle market’ inda dubban masu safarar shanu, raguna, rakuna da ke tasowa daga kasashen Togo, Chad da Mali ke haduwa.
Shugaban kaswuar, Bashir Zubairu, ya bayyana cewa, “kasuwar ta kadu da kulle iyakokin, don a yanzu ba za a iya shigo da kayayyaki ba saboda kulle iyakokin da aka yi.
Wani dan siyasa kuma dan kasuwa Alhaji Mijinyawa Auta, da ke harkokkin zirga-zirgar manyan motoci daga Sakkwato zuwa Niamey ya nema shugananin kasashen ECOWAS su kai zuciya nesa, su janye Shirin kai hari a kan kasar Nijar, musamman ganin halin da za a jefa al’umma a ciki in har haka ya faru.
Bayanai suna cewa, kasar Nijar ta fusata da kungiyar ECOWAS musamman Nijeriya. Kaste wutar lantarki daga Nijeriya ya jefa kasar cikin mawuyacin halin da basu taba gani ba a baya.
“Lamarin ya munana, asibitoci basu iya gudanar da aiki ga marasa lafiya amfani da janareta yana da matukar tsada musamman ganin tsadar man fetur da ake fuskanta a halin yanzu.
An kulle hada-hadar kudade a tsakanin kasashen ECOWAS da Nijar kuma gashi sun dogara da Nijeriya ne wajen samun abinci kuma gashi an kulle iyakokin kasar da Nijeriya gaba daya,” in ji sanarwa.
Shugaban kungiyar masu aiki da hukumar Kwastam a Jihar Sakwatto, Alhaji Aminu Dan’Iya, ya ce mambobinsa da suka kai fiye da mutum 100 sun rasa ayyukan su tun da aka kulle iyakokin Nijeriya da Nijar.
Al’ummar da ke zama a yankunan Geidam da Mainesorowa da ke a kan iyakar Nijeriya da Nijar a Jihar Yobe sun bayyana cewa, takunkumin da aka sanya musu sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar ya tsayar da dukkan harkokin kasuwanci a yankin gaba daya.
Da wakilinmu ya ziyarci Geidam-Mainesorowa, a iyakar Nijeriya da Nijar musamman kauyuka kamar, Abbari, Bature-Wango, Bula-Barnaye, Garin-Gada, Ngomari da Adjuri al’umma yankin sun bayyana yadda rufe iyakokin ya shafi harkokin kasuwancinsu da na yau da kullum.
Shugaban ‘yan kasuwan garin Geidam, da ke jihar Yobe, Alhaji Abdulrashid Abba, ya bayyana cewa, kai harin soja kasar Nijar zai kara ta’azara halin matsin da ake ciki ne a yankuna da harkokin ta’addancin Boko Haram ya riga ya jefa cikin mummunan hali.
“A matsayinmu na al’ummar da ke wa yankin iyakokin Nijar da Nijeriya ba mu yarda da daukar matakin soja a kan Nijar ba. Da aka yanke shawarar ECOWAS za ta dauki matakin soja a kan Nijar, mu 14 daga cikin shugabannin kungiyar mun nuna rashin amincewarmu a kan shawarar musamman ganin tun daga yankunan Damagaram da Kegime da ke kasar Nijar duk a lardin kasar Kanem Borno suke a kan haka dukkan mu daya ne babu bambanci.
“Saboda kulle iyakokin ledar ruwa da ake sayarwa a kan kasa da naira 300 a halin yanzu ya kai fiye da naira 500. Ya kamata shugaba Bola Tinubu da kungiyar ECOWAS su fahimci cewa bamu gama fita daga kangin ‘yan ta’addan Boko Haram ba don haka kada a tayar mana da wani rikicin kuma a halin yanzu”.