• English
  • Business News
Friday, October 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Takaitaccen Bayani Kan Dashen Dogon-yaro Da Lokacin Amfaninsa

by Abubakar Abba
2 years ago
Dogon Yaro

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

Bishiyar Dogon-yaro na fara fitar da ‘ya’ya ne daga shekaru uku zuwa biyar, inda kuma ta ke kammala girma a cikin tsawon shekaru goma.

A duk shekara bishiyar na samar da ya’ya’ da yawansu ya kai kimanin kilogiram 50, haka zalika; bishiyar na shafe dimbin shekaru a duniya ba tare da komai ya same ta ba.

  • Sin Na Goyon Bayan Yunkurin IAEA Na Tabbatar Da Tsaron Tashar Nukiliya Ta Zaporizhzhia
  • Ana Gudanar Da Horo Kan Gina “Koren Babbar Ganuwa” A Afirka A Beijing

Zuwa Tsawon Wane Lokaci Irin Dogon-yaro Ke Kammala Girma?

Irin Dogon-yaro na da gajeriyar rayuwa; ba ya yin tsawon kwana, domin kuwa yana kai wa daga kwana 10 ne zuwa 12 a lokacin da yake a danyensa. Don haka, ana so ka tabbatar da ka samu ingantaccen Irin da zai yi saurin nuna bayan shuka shi.

Haka zalika, ana so a tabbatar an rufe shi a cikin Tukunya; domin ya kasance ya na samu lema, wanda hakan kan taimaka masa daukar tsawon kwanaki ko mako uku, bayan shuka shi.

Wacce  Kasa Ce Aka Fi Samun Bishiyar Dogon Yaro?

A bisa rahotannin masana a kan harkokin kimiyya da fasaha da kuma binciken da cibiyar bunkasa aikin noma ta kasa da kasa suka gudanar a shekarar 1992 sun bayyana cewa, an fi shuka bishiyar Dogon-yaro a bangaren Asiya da Nahiyar Afirka da kuma wasu kasahe na fadin duniya.

Har wa yau, kusan kashi 60 cikin 100 na al’ummar da ke Kasar Indiya; na shuka wannan bishiya ta Dogon-yaro.

Wace Irin Kasar Noma Bishiyar Dogon-yaro Ta Fi Bukata?

Bishiyar Dogon-yaro ta fi bukatar kasar noma mai inganci, sannan kuma ba a so a shuka Irin a wajen da ruwa ya ke yawan zama.

Wane Bangare Na Bishiyar Dogon-yaro Ne Ake Amfai Da Shi Wajen Sarrafa Magunguna?

Baya ga ita bishiyar ta Dogon-yaro, ana kuma amfani da ganyenta da Irinta da kuma jikinta wajen sarrafa magungunan gargajiya.

Yaya Ake Adana Ganyen Bishiyar Dogon-yaro Ya Dauki Tsawon Lokaci?

Da farko dai, za ka ciro wannan ganye daga jikin wannan bishiya ta Dogon-yaro.

Sannan, matali na biyu kuma ana so ka zuba ganyen a cikin kwano, sai ka rufe shi domin ya tsotse Lemar da ke jikinsa; sannan kuma sai ka rufe shi.

Mataki na uku kuma shi ne, saka shi a cikin firji ko na’ura mai sanyi.

Yadda Ake Tatsar Man Dogon-yaro Daga Ganyensa

Ana bukatar a nika shi, sannan sai a dora shi a kan wuta a tafasa shi ya dauki kamar minti 15, bayan ka sauke shi daga wutar sai ka bar shi ya yi kamar awa biyu ko sama da haka.

Daga nan, sai ka adana shi a wurin da yake a bushe; kana kuma ka tabbatar da cewa, rana ba ta kai ga inda yake ba.

Ana Samun Dimbin Kudaden Shiga A Noman Bishiyar Dogon-yaro

A yanzu haka, bishiyar Dogon-yaro na kara samun karbuwa a fadin duniya, musamman ganin yadda fannin ke samar da kudaden shiga masu daman gaske, haka nan kuma akwai masa’antu da ke sayen sa; domin sarrfaa shi zuwa wasu nau’ikan abubuwa da dama kamar: magunguna, man shafawa da sauran makamantansu.

Har ila yau, bishiyar Dogon-yaro na jurewa fari; sannan kuma bishiyar ta fi son yanayin da bai wuce 21°C zuwa 32°C ko kuma  70°F ko 90°F.

Bugu da kari, wani kwararre a fannin wannan noma na bishiyar Dogon-yaro, Dakta Abdullahi Ahmed Yar’adua ya bayyana cewa,  lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali wajen bunkasa noman Dogon-yaro fiye da yadda Kasar Indiya ke yi a halin yanzu.

Dr Yar’adua ya tabbatar da cewa, Indiya na da kimanin bishiyar Dogon-yaro da suka kai kimanin miliyan 20, inda ya kara da cewa; daga shekarar 1985 zuwa  1995, gwamnatin kasar na samun kudaden shiga da suka tasamma kimanin dala biliyan 2.5 daga man da take samu daga wannan bishiya ta Dogon-yaro.

Sannan ya sanar da cewa, ana sarrafa ganyen wannan bishiya wajen sarrafa takin zamani, inda ya dora laifin yadda fanin ke samun koma baya a kan yadda shugabanin kasar nan ko kadan ba sa mayar da hankali kan noman Dogon-yaro.

Haka zalika, ya kuma koka a kan yadda aka yi watsi da masa’antar noman Dogon-yaro, wadda tsohuwar gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo ya kafa a Jihar Katsina.

Dr Yar’adua ya kuma shawarci gwamnati ta mayar da hankali wajen noman bishiyar Dogon-yaro, musamman ganin yadda ake samun kudaden shiga masu masu dimbin yawa a sauran kasashen duniya daban-daban.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI
Noma Da Kiwo

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
Next Post
An Damke Wasu ‘Yan Nijeriya Kan Zargin Tilasta Wa Dan Australiya Tura Masu Hotuna

An Damke Wasu ‘Yan Nijeriya Kan Zargin Tilasta Wa Dan Australiya Tura Masu Hotuna

LABARAI MASU NASABA

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

October 24, 2025
Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 

Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 

October 24, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe

October 24, 2025
Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu

Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu

October 24, 2025
Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu

Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya

October 24, 2025
Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi

October 24, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule

October 24, 2025
Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.