Sadiya Umar Faruk ‘yar siyasa ce a Nijeriya, ta taba rike mukamin Ministan Kula da Jin Kai da Kula da Bala’o’i da Ci Gaban Al’umma.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya nada ta a watan Yulin 2019. Sadiya Umar Faruk ta kasance minista mafi karancin shekaru a majalisar ministocin tarayya wadda ta shude. Ta yi aiki a matsayin kwamishiniyar Tarayya ta Hukumar ‘Yan Gudun Hijira, baki da mutanan cikin gida (NCFRMI) daga Oktoban 2016 zuwa Agustan 2019.
Aikinta da shugaba Muhammadu Buhari ya samo asali ne tun zamanin da Buhari na matsayin shugaba kuma dan takarar shugaban kasa na rusasshiyar jam’iyyar ‘Congress For Progressibe Change,’ (CPC) lokacin da Sadiya ta kasance ma’ajin jam’iyyar CPC ta kasa sannan kuma ma’ajin jam’iyyar All progressibes Congress APC.
Sadiya Umar Faruk ta samu nasarori da dama tun lokacin da aka kafa ma’aikatar jin kai da kula da bala’o’i a watan Agustan shekarar 2019, ya zuwa yanzu akalla ‘yan Nijeriya miliyan 20 ne aka bai wa tallafi ta hanyar tsare-tsare na zamantakewar al’umma daban- daban da tsare-tsare na ma’aikatar.
Haka nan kuma an bayyana cewa, a karkashin shirin ciyar da makarantu na gidauniyar, jimillar yara miliyan 9.9 daga firamare 1 zuwa 3 a makarantun gwamnati a duk fadin kasar, ana ciyar da abinci mai zafi a duk rana, inda dalibai 126,000 ke cin gajiyar girkin.
A zamaninta ta inganta wa ma’aikatar ta samu damar sama wa matasa kusan 1,664,774 da shirya- shiryen da suka kammala karatu da wadanda ba su kammala karatu ba a karkashin shirin N-power.
A farkon watan Yulin 2022 Sadiya Umar Faruk ta ba da sanarwar bayar da tallafin tsabar kudi ga marasa galihu a Oshogbo, Jihar Osun.
A matsayinta na mai girma minista tana ba da jagoranci a cikin ci gaban manufofin jin kai da ingantaccan hadin kai na ayyukan agaji na kasa da kasa: tabbatar da dabarun magance bala’i, shirye-shirye da amsawa da gudanar da tsarawa da aiwatar da shirye-shiryen hadaddun jama’a da tsare-tsare na adalci a cikin Nijeriya dai dai da ma’aikatar.
Kafin nada ta a matsayin minista Sadiya Umar Faruk tana da tarihi a matsayin mai girma Kwamishiniyar Tarayya Ta Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira Da Bakin Haure (NCFRMI).
Ta fito da wani Sabin taswirar dabarun aiki don sake mayar da hukumar don daukar nauyin jagoranci a matsayin kungiyar jin kai ta Nijeriya da kuma kawo ayyukan hukumar zuwa matsayi a duniya.
Sabuwar taswirar dabarun hukumar ta mayar da hankali ne kan samar da mafita mai dorewa ga wanda abin ya shafa tare da jaddada kayyadaddun hanyoyin yin amfani da bincike, tattara bayanai da tsare-tsare don sake saitawa, gyarawa, sake hadawa, da sake dawo da duk mutunen da suka cika a cikin hukumar.
Ofishinta yana aiki hannu da hannu da hukumar kula da nakasassu ta kasa, karkashin jagorancin mista James Lalu, don tabbatar da hada nakasassu fiye da miliyan 30 a cikin al’amura da suka shafi kasa da jama’arta. Don haka ta kaddamar da cibiyar samar da takaddun Lantarki na Nakasassu da ke cibiyar masu nakasa da ke Abuja.
Sadiya Umar Faruk an haife ta 5 Nuwamba 1974, shekarunta sun kasance 48 kenan, ‘yar garin Zurmi ce dake Jihar Zamfara.
Sadiya Umar Faruk ta auri shugaban hafsan sojan sama tana matsayin minista a watan satumba 24 shekara ta 2020.
Sadiya Umar Faruk ta yi fatali da jita-jita ko kuma labaran karya game da auren shugaba Buhari.
Ministan agaji da agajin gaggawa da masifu da cigaban jama’a Sadiya Umar Faruk ta mika ayyukan ma’aikatar ga babbab sakataren dindindin Dakta Nasir Sani Gwarzo mni. NPOM, bayan shekaru uku da rabi da ta yi tana kyakkyawar hidima ga bil’adama da kuma karshen zamanta a matsayin ministar majagaba.
Sadiya Umar Faruk ta mika takardun da ke kunshe a cikin litattafai guda biyu, na aikinta a ma’aikatar, a karshen taron jin kai na Nijeriya karo na daya da ma’aikatar ta shirya a ranar juma’a a Abuja.
A nata jawabin, ministar ta godewa babban sakatare, daraktoci, ma’aikatan ma’aikatar da kuma Ofishinta bisa dimbin tallafin da aka ba ta a tsawon lokacin da take rike da mukamin.
Sadiya Umar Faruk ta bukaci ma’aikatan da su jajirce wajan ganin sun cimma burin shugaban kasa Muhammadu Buhari na fitar da masu karamin karfi daga kangin talauci.
Na mika wadannan takardun aikin a hukumance a matsayina na majagaba a ma’aikatar jin kai da ci gaban bala’o’i da ci gaban al’umma a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata.
Na gode kwarai da goyon bayanku ya yin da ta mika wa babban Sakatare, Dakta Nasir Sani- Gwarzo.
Da ya ke mayar da martani, Sakataran dindindin ya godewa ministar tare da yi mata fatan alheri a ayyukanta na gaba.
Ministan ta ce ma’aikatar ta ta ta samu damar kara wa rayuwar marasa galihu da iyalansu kima a cikin shekaru hudun da suka gabata kuma da kara yin wani abu da za ta iya kai wa ga gidaje da dama a Nijeriya amma ta yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya ke da hangen nesansa wajen samar da sabuwar hidima.
Ministan ta sanar da cewa a cikin tsawon lokacin da ake bitar ma’aikatar ta samu damar tsarawa da aiwatar da shirin ciyar da abinci na gida-gida na kasa, wanda a kullum ke samar da abinci mai gina jiki ga dalibai 9,990,862 a jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja tare da samar da ayyukan yi ga kasa da kasa.
A lokaci guda kuma Sadiya ta ce a kalla mutane 1,940,325 marasa galihu da aka zabo daga dukkan sassan Nijeriya suna samun tallafin kudi na Naira 5000 duk wata a karkashin shirin ma’aikatar da ke ba da tallafin kudi na musamman, wanda kuma ke samun tallafin Bankin duniya.