Connect with us

SIYASA

Takarar Abdulrahman Kawu Sumaila Alkhairi Ne Ga Al’ummar Kano Ta Kudu -Dini Falalu Fagge

Published

on

An bayyana takarar Sanatan Kano ta kuda da mai baiwa shugaban kasa shawara akan majalisar wkilaai ta tarayya Abdulrahman Kawu Sumaila ya fito da cewa ta dace d muradun al’ummar Kudancin kano da jihar Kano bakai daya.
Wani matashin Dan siyasa a jihar kano Dini Falalu Fagge ya bayyana hakan tareda cewa yanada yakinin Kawu Sumaila zai zama wakili dazai kare muradun al’ummar yankin muddin yakai ga nasara duba da irin abubuwa da yayi na ci gaban al’uma yankin da jihar Kano baki daya.
Dini Falalu Fagge ya ce ko lokacinda Kawu Sumaila ya wakilci mazabun Takai da Sumaila a majalisar wakilai a baya yayi rawar gani sosai wajen kawo kuduri da samarda ayyuka na ci gaban yankin.
Yayi nuni da cewa Kawu sumaila a lokacinda ya zama shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta tarayya yayi iya kokarinsa wajen kare martabar al’ummar jihar kano dana arewacin kasar nan.
Dini Falalu Fagge ya ce irin wannan kishi na al’umma da taimaka musu da yake tasa ake ganin zai iya kawo ci gaba da wakilci nagari ga yankin kano ta kudu.
Ya ce al’ummar Kano ta kudu za su gane cewa a yanzu ne za su sami wakilci mai ma’ana idan suka tura mai kishin ci gabansu duba da irin kokawa da suke na koma baya na tsawon lokaci.
Dini Falalu Fagge ya ce sun san kawu Sumaila mutumne da yakeda kauna ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan jihar Kano wanda koda yaushe za ka ga yana tallata manufofin Gwamnatin APC da kuma yin duk abinda yakamata dan ganin an samarda ci gaba ga al’ummar jihar Kano.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: