Abokin takarar Bola Ahmed Tinubu a jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023, Kabiru Ibrahim Masari, ya shaida Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa (INEC), cewar shi ma kafatanin takardun makarantarsa sun bata.
Masari ya nuna wa INEC takardar shaidar batan takardun nasa da ya yi a kotu; ciki har da takardar shaidar kammala karatun Grade II, da ya yi a Jihar Katsina.
- An Yanke Wa Dan Sandan Da Ya Kashe Direban Bas Hukuncin Kisa
- Dole Ne A Ci Gaba Da Binciken Alkalin Alkalai Mai Murabus, Tanko Muhammad — Majalisa
“Wani lokaci a Janairun 2021, a kan hanyata a yankin Wuse a Birnin Tarayya Abuja, na gano cewar kafatanin takardun makaranta ta sun bata, wanda hakan ya sa na yi takardar shaidar batansu a kotu, kuma na mika ta ga INEC a ranar 17 ga watan Yuni, 2022.
“Duk kokarin da na yi don gano inda suka shiga ya ci tura, amma ina da shaidar takardar kotu,” a cewarsa.
Yana daga cikin sharudan dokar zabe ga ‘yan takara da su gabatar da shaidar takardun karatunsu ga INEC a lokacin tantancewa don bayyana su ga jama’a gabanin shiga zabe.
Idan ba a manta ba, Tinubu ya bayyana wa INEC cewar takardunsa na Firamare da Sakandare sun bata, lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin masu sharhi kan al’amuran siyasa.
A ranar Asabar ne Tinubu, ya ce ya zabi Masari ne a matsayin wanda zai masa takara amma ta wucin gadi, wanda a cewarsa yana ci gaba da neman wanda zai yi masa abokin takara na dindindin.
Sai dai kuma zabar Masari a matsayin Musulmi, wanda hakan ke nuna Musulmi biyu za su takarar shugaban kasa da mataimaki, ya tada kura musamman ga yankin Kudu Maso Gabas na kasar nan.