Huzaifa Dokaji" />

Talaka Bawan Masu Gari

arabiandokaji@gmail.com   08180897610

Lallai wani abu na kusa da faruwa a kasar nan, ko dai talaka ya tashi ya kawo karshen zaluncin da ake masa, ko kuma zalunci da ake masa ya karu. Sai dai akwai kyautata zaton zaluncin ne zai ci gaba da karuwa saboda dalili biyu. Na farko, juyin juya hali na faruwa ne idan al’amura suka fara daidaituwa amman ba sa tabbata da sauri yadda ake bukata. Komai a kasar nan kara tabarbarewa yake, ba ga tsaron da ake murna ya samu ba, ba ga abinci ko muhallin zama ba. Dalili na biyu kuma shine, a kullun a kasar nan talaka rage hankali yake a filin siyasa da zabe. Wannan rashin zurfin tunani na talaka ya kai ra’ayin talaka na zabe ya kai matakin nan da Karl Mard ke cewa ‘duk shekara hudu talakawa na haduwa su zabi jerin mutunen da za su ci gaba da zaluntarsu’.

Hangen nesan talaka ya zama abin jimami da Allah wadai. Hankalin mutum ba zai tashi ba har sai ya fahimci cewa wai fa maimakon ya’yen masu kudi su zama su ne suke kare iyayensu akan zaluncin da su ke, dan talaka ne yake kashe kudinsa ya shiga yanar gizo, ya caja wayarsa da injin da ya sa fetur mai tsada ko kuma ya biya a wajen mai caji, sannan ya hau ya kare masu zaluntar ta sa! Lallai Malam Sa’adu Zungur yayi gaskiya: ‘wagga al’umma me za ta wo a cikin zarafofin duniya’! Ban sani ba dai, amman a ganina ba’a taba talakan da ake zaluntarsa yake kuma taimakawa a zalunce shi ba irin na kasar nan. Banda dai dan kasar nan dan kasar nan ne, ya mutum zai dau maka alkawaruka, ya banzatar da kai, ba zaka kuma ganin shi ba sai zabe ya gabato amman kuma ka ci gaba da tada jiniyar wuya a kanshi? Rana guda saboda zabe ya zo daga kaga wannan dan siyasar ya zama lebura sai kaga wannan ya yanko hanya da talakawa yana shan rake, wai shi na su. An mayar da talaka tiski

Masifar da ake ciki a kasar nan ta kai wai ayi amfani da talakan da banda cutarsa ba abinda Turawan Yamma da yan barandansu ke yi a rufe bakin masu kokarin fadar ko tabbatar da an daina zaluntarsa. A biya shi kudi, ya sace, ya razana ko ya kashe mutanen da sun fi shi amfani. To wai ranar da masu cutar mu suka yi nasara masu fahimtar ana cutarmun suka kare, malam talaka ya zai yi? Lallai akwai bukatar talaka ya fahimci cewa ba fa shi da wata mafita da ta wuce ya kama abokin shan wahalarsa hannun bibbiyu su nemi mafita. Dan kasar Isara’ila ba zai taba hada kai da dan Falasdinu a cuci abinda ya shafi kasarsa ta Isra’ila ba, wannan sai dan Afirka, dan Afirkan ma dan Nijeriya, dan Nijeriyar ma sai… Na dai yi shiru! Amman dai baitin da Malam Mu’azu Hadeja ya fasalta Bahaushe da shi, na so talaka gaba daya ya siffanta da su. Sai mu din ga cewa:

Talaka mai ban haushi,

Na Tanko mai kan bashi

Da ba ruwansa da kishi

Sai dai a san mai dashi

Bashi son dawainiya/

Babba! A gaida saraki-

Babu sana’ar kirki

mai kwazo wajen biki-

Sai a yi rokon baki

Don neman abin miya

Babu wani abu da yake tafiya daidai a kasar nan banda rashin sanin ya kamata a tsakanin mahukunta da talakawa. An kafa gwamnati wadda talaka ya dora buri a kanta kamar zuwan Mahadi. An dau alkawari kamar an so a cuci budurwa, sai dai fa har zuwa yau banda tsaro da aka kamanta abinda ya kamantu a inda zai kamantu, babu wani abin a zo a gani da talaka ke mora. Ilimi na halin da yake ciki na rashin kyau, babu wani canji da aka samu. Makarantunmu babu wani canjin a zo a gani da aka samu. Har yau ‘yan kasar nan ba su fara morar wani tsari da zai sama musu ma aikin yi ba. An kawo tsarin N-Power, wanda idan aka duba da kyau wata dabara ce ta dauke hankalin dan talaka daga neman aiki a ma’aikatun da ya’yen masu kudi kadai ke samunsu. Su bamu N-Power, su kai ya’yensu FIRS, PENCOM, NCC da irinsu NDIC inda ake biyan albashi, kamar yadda wani kakana yake fada, mai sa murmushin ba shiri. Kana magana a ce Buhari ya ce a koma gona! Kai sai ka ramtse da Allah kasashen da suke amfanar noman, da fatanya da lauje suka kawo ci gaba. Babu kayan noman zamani, me zaka noma? Sun sace kudin takin, sun ki bada motocin noma sun ki yi kwalta, ina noma za ta inda ake so? Ba ruwan talaka! Shi dai sai dan amarya!

A matakin tsaro dole za’a yabawa gwamnati wajen dakile hare-haren rashin hankalin da a baya suka gallabi kasar nan. Sai dai fa akwai lauje a cikin nadi idan muka duba cewa rashin tsaron na nan, salo da muhalli kawai ya canja. Maimakon bama-bamai, yanzu harbe da yanka mutane ake. Wai a kwantar da Dan Adam a yanka, sai ka ce wata akuya! Kai! Wani aikin sai talaka! Kullun a shafukan jarida sai mutum ya karanta an kashe mutane, mun ma saba ba ma jin wani tashin hankali akai. Da kudin man fetur aka kara da watakila yanzu mun kashe titinan kasar nan da zanga-zanga. Ga abin zanga zanga nan kuma ba ruwan mu, ko da yake ai gwamnatin dan amarya ce! Dan amarya ba ka laifi! Akwai matsala kwarai a ce soyayya ta rufe idanuwan mu daga ganin wannan tashin hakali da ake ciki, kawai saboda mu bala’in ya bar kofar gidajen mu ya koma na wasu, ko kuma saboda kar mu ai bata namu, tunda wasu basa aibata na su, ko kuma saboda dai kawai muna bayan dan Amarya.

Babu soyayyar da ta wuce ka fadawa naka gaskiya, ba don ka tozarta shi ba, sai dai dan ka nusar da shi hadarin da yake jefa kansa da kuma wanda yake jefa ka. Duk kyakkyawar niyyar da shugaba ke da ita fa, matukar bai amfani da ita wajen amfanar talakawansa ba, ba ta da wani amfani, gara kashin safe da ita. Ina amfanin gaskiyar shugaba ya bari ana sace kudin al’umma kuma baya daukan matakin da ya kamata akai? Ina amfanin kishin shugaba yana zama da barayi, matsawar barayin masu dadadada ransa ne? Ina anfanin rashin tsoron shugaba idan ba zai iya amfani da shi ya yakice mugaye daga cikin tafiyarsa ba? Shugaban mu ya gaza, akwai bukatar mu tashi tsaye haikan mu nusar da shi hakan, mu kuma dafa masa ya gyara. Sai dai fa ba yadda zai zama ma’anar da mu ka bawa barawo da mu da shi ta banbanta. Ya za’ace in dai dan siyasa yana wuridin “sai Baba” shi mai gaskiya ne wanda kuma yake wuridin “baba ya gaza” shi kuma shine barawo.

Duk sanda aka kwafsa sai a zo da uzurin ai PDP ce ta lalata kasar nan, kamar dama basanin hakan ne yasa muka koreta mu ka kawo APC su gyara mana ba kenan! Idan fadar itace ta lalata kasar ba tare da an wani yunkurin gyarawa ba muke so, ai ba sai mun kawo wani ba domin mun jima da fadawa duniya hakan. Akwai tashin hankali kwarai idan ni da nake zama a kan dakali a umguwa in zagi PDP akan cutar kasar nan da ta yi ace wai shugaban kasa ma babu wani da zai in ba hakan ba! Mun yarda PDP ta lalata kasar nan, to me APC take domin ta gyara? Shin duk ranar da muka sha wajen zaben Buhari, duk cin mutuncin da mukai wa sarakunan mu na gargajiya da wasu daga malamanmu, yi mukai dama don idan an hau an gaza a dame mu da uzurin su su ka lalata kasar nan?

An fitar da jerin sunayen wadanda suka sace kudin kasar nan, amman babu suna barayin jirgin ruwan fetur a ciki, babu sunan dillalin ciyawa, babu sunan barayin da suka sace kudaden jihohinsu suka marawa dan amarya baya yaci zabe! Zabe dai na gabatowa. Ya kamata duk wanda ya kuma fitowa ya ce mu zabe shi ya sanar da mu abinda ya yi mana. Idan ya dau alkawari mu tabbatar ya cika. Babu dalilin da zamu rika zabar mutanen nan su rika wasa da hankalin mu kamar ‘yan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na gwada kwarewarsu ta tiki-taka.

Exit mobile version