Shugaban hukumar jin dadin alhazai na kasa (NAHCON) Alhaji Zikrullah Hassan, ya koka akan yadda talauci ya sa wasu ‘yan Nijeriya ke yin barace-barace a kasashen waje musamman a kasar Saudiya.
Zikrullah a Jawabinsa a wani taro karo na bakwai na Gidauniyar bankin Jaiz da Bayar da zakka da aka gudanar a Abuja, ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a kawar da talauci a tsakanin ‘yan kasar nan, musamman ta hanyar samar musu da sana’oin hannu maimakon yin barace-barace.
Ya yaba da kokarin Gidauniyar akan ayyukan da take gudanar wa ga jama’a don rage musu radadin talauci, inda ya ce, ta hanyar bayar da Zakka za a iya yakar talauci.
Shugaban Gidauniyar Mallam Adamu Bello ya sanar da cewa, ta hanyar bayar da Zakka, za a iya sharewa Musulmai kukansu na kalubalen rayuwa da suke fuskanta na yau da kullum.
Shi kuwa babban jami’in a Gidauniyar Dakta Abdullahi Shuaib ya ce, an rabar da zakkar kudi naira miliyan 18,985,439 ga mutane 202 a babban birnin tarayyar Abuja.
Dakta Abdullahi ya kara da cewa, an raba zakkar kudi a wannan shekarar ga mutane 625 har naira miliyan 59,949,439 a cikin jihohi shida har da Abuja.
Ya yi nuni da cewa, talauci ya jefa rayuwar jama’ar kasar nan a cikin mawuyacin hali duk da irin kokarin da gwamnati ke yi na kokarin kawar da talaucin.