Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da wata kididdiga da ta nuna talauci ya karu a Nijeriya da kashi 14 a cikin 100.
Ta bayyana cewa farashin kayayyakin da ake amfani da su tare da nuna cewa an sami hauhawan farashi da kashi 17.81 a watan Mayu idan aka kwatanta da watan Afrilu da aka sami kashi 16.82 a wannan shekarar duk da yake ya ragu ne a kan abun da aka samu a watan Mayun shekarar da ta gabata ta 2021 da aka sami kashi 17.93.
Talaudci da kuncin rayuwa a cikin kasa na ta karuwa bisa alamu wanda lamarin ba Nijeriya ba ne kawai duk duniya ne. Bankin Duniya daga baya-bayan nan ya haskako karuwar kuncin rayuwa kusan ilahirin kasashen duniya za su fuskanci wannan matsalar.
Bankin Duniya ya bayyana cewa habakar tattalin arziki ya yi kasa da kashi 2.9 cikin dari daga kashi 5.7 cikin dari da aka hassaso a shekarar 2022. Shugaban Bankin Duniya, Dabid Malpass ya yi gargadin cewa yakin Ukraine da annobar Korona da ya janyo rufe China waDanda suka janyo tashin farashin abinci da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum su suka shafi tattalin arziki.
Idan aka duba kyau za a ga cewa kuncin rayuwa ba Nijeriya ne kadai ba, ko’ina ne a duniya, akwai kasashe sama da 25 a duniya da suke da kuncin rayuwa. Alal misali Turkiyyya tana da kuncin rayuwa da kashi 73.5 cikin 100, a yayin da yaki ya kara kuncin rayuwa a Sudan ya karu da kashi 192.2 cikin 100.
Rasha da Ukraine kuncin rayuwa ya karu da kashi 18 da 17 cikin 100, idan aka dawo nan Afrika kuwa, Ethiopia yana da kuncin rayuwa ya kai kashi 37.7 cikin 100. Ghana da Angola da Sierra Leone sun kai kashi 27.6 da 23.42 da 22.44 cikin 100 na kuncin rayuwa.
A lokacin da yake magana kan ci gaba da kuncin rayuwa, Mataimakin Gwamnan babban Bankin Nijeriya a fannin tsarin tattarin arziki, Kingsley Obiora ya ce tattalin arzikin duniya yana tafiya ne cikin wani mawuyacin hali.
Ya ce, “Mun ga yadda farashin kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi musamman abinci da muke amfani da shi, sakamakon rikicin Ukraine da Rasha wadanda suke fitar da kayayyaki.
“Mun ga yadda harkokin kasuwannin duniya ta kasance bayan rufe China da aka yi wanda duk mun san wadannan nan a yanzu su ne suke samar da abubuwa a duniya. Mun ga yadda ake kokarin daidaita bukatuwar abu, kuma wannan dalilin ne ya haifar da tsadar kayayyaki.
“Mun kuma ga yadda aka rasa ayyukan yi a duniya don wasu sun zabi su yi aiki daga gida. Dukkanin wadannan abubuwa su ne suka haifar da kuncin rayuwa a duniya. Za ka iya zuwa Burtaniya da Amurka a baya can babu kuncin rayuwa, amma a yanzu sun shiga ciki.
“A yanzu a Burtaniya suna da kashi 6 cikin 100, a yayin da Turai ake da kashi 9 cikin 100. Idan kuwa aka je Argentina alal misali, suna da kuncin rayuwa sama da kashi 70 cikin 100. Amma idan muka duba a Nijeriya idan muka kwatanta da sauran duniya za mu iya cewa muna da kashi 17 cikin 100 ne kawai.
A lokacin da yake sharhi kan kuncin rayuwar da Nijeriya ke ciki a halin yanzu, kwararren mai sharhin al’amuran yau da kullum a FDTM, Lukman Otunga ya bayyana cewa akwai lokacin da Nijeriya ta yi shiru a kan shiga wani kuncin rayuwa da aka yi.
Ya ce, “A daidai lokacin da wasu kasashe a duniya suke kokarin duba farashin kayayyaki, kasar da ta fi kowacce kasa girman tattalin arziki a Afrika kuma take da masaniyar yadda za ta sassauta kuncin rayuwa. Wannan dabara ce da CBN ya gaza sauya shi wajen inganta tattalin arzikin kasa da habaka shi.
“A yanzu kuncin rayuwa a Nijeriya ya karu sosai a watanni hudu a jere zuwa kashi 17.71 cikin 100 a watan Mayu.
Wanda za a iya cewa shi ne mafi muni tun daga watan Yunin bara, hakan ya sanya aka sami karin farashin abinci da farashin man dizil da kuma karancin dalar Amurka.
Wannan kuma shi ne yadda kayayyaki suke kara tashi a duniya da shirye-shiryen zabe wadanda su ne abubuwan da suke kara tsananin matsalolin da ake fuskanta.
Musamman bayan kalaman da hukumar IMF ta yi game da farashin kayayyaki, inda ta ce zai tashi daga tsakanin kashi 18 da kashi 22 cikin 100 a shekarar 2022.