Gwamnatin Taliban a Kasar Afghanistan ta sanar da haramta wa dalibai mata karatun jami’a, a wani sabon mataki da ta dauka da ya shafi daukacin jami’oin gwamnati da masu zaman kansu.
Wata sanarwar da ma’aikatar ilimin kasar ta gabatar ne, ya bayyana daukar wannan sabon mataki na haramta karatun jami’a ga daliban mata na har illa masha Allahu.
- Babu Matakin Da Muka Dauka Kan Murabus Din Okupe – Kwamitin Yakin Zaben Peter Obi
- Abokan Hamayyata Ba Su Da Nagarta – Tinubu
Mai magana da yawun ma’aikatar ilimin Ziaullah Hashimi, ya gabatar da wannan sabuwar doka, wadda ake ganin za ta dakushe aniyar dalibai mata na samun ilimi a cikin kasar.
Haramcin karatun a jami’oin Afghansitan na zuwa ne kasa da watanni uku bayan dubban dalibai mata sun zana jarabawar shiga jami’a a fadin kasar, yayin da wasu suka gabatar da takardun neman kwarewa a bangaren Injiniya da kuma zama Likita.
Bayan karbe iko da Afghansitan a watan Agustan bara, Taliban ta bai wa jami’oi umarnin aiwatar da sabbin dokoki da suka kunshi raba maza da mata a azuzuwa, yayin da aka bai wa malamai mata damar koyar da dalibai mata kawai.
Rahotanni sun ce tuni gwamnatin kasar ta haramta wa dalibai mata da dama karatun sakandare, abin da ya taikaita yawan daliban da ke samun damar zuwa jami’a.