Sharafaddeen Sidi Umar" />

Tambuwal Ya Bayar Da Kwangila 200 A SUBEB

A hobbasar kwazonsa na kara inganta sha’anin ilimi a Jihar Sakkwato, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da sababbin kwangila 200 a Hukumar Bayar Da ilimi Bai Daya ta Jiha (SUBEB) domin gina makarantu da sauran ayyukan bunkasa sha’anin ilimi.

Ayyukan wadanda suna daga cikin ayyukan Hukumar Bayar Da Ilimi Bai Daya na 2018/2019 na da manufar tayar da komadar sha’anin ilimi da tabarbarewar da ya yi a Jihar wanda shine dalilin da yasa bayan shigarsa ofis a 2015 ya kafa dokar daukin gaggawa a sha’anin ilimi.

A jawabinsa a wajen taron bayar da takardar fara aiki ga ‘yan kwangila 200 a ranar Lahadi, Gwamna Tambuwal ya bayyana cewar Gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai wajen inganta sha’anin ilimi wanda shine ke da kaso mafi yawa a Kasafin Kudin Jihar a kowace shekara a mulkinsa.

Ya ce wadanda suka amfana da samun kwangilar 200 za su fara aiki ne a nan take ba tare da bata lokaci ba tare da kira gare su da su gudanar da ingantaccen aiki kwatankwacin yadda aka umurce su domin duk dan kwangilar da ya yi aiki marasa inganci Gwamnati za ta dauki mataki.

Gwamnan ya ce an kashe sama da naira bilyan 11 wajen gina makarantu, ajujuwa da ofisoshin malamai da kayan aiki a makarantu daban-daban a Birnin Jihar da daukacin Kananan Hukumomi 23 da ke fadin Jihar da manufar ganin ya canza fasali da alkiblar sha’anin ilimi a Jihar.

Exit mobile version