Sharfaddeen Sidi Umar" />

Tambuwal Ya Yi Fatan Samun Nasarar PDP

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewar Nijeriya na bukatar kara himma domin ganin zabukan da za a gudanar a gaba sun fi wadanda ake gudanarwa yanzu inganci.
Ya ce idan har za a daga zaben 2015 saboda matsalar kayan aiki kamar yadda Hukumar Zabe ta bayyana kuma a sake samun irin wannan matsalar a 2019 akwai bukatar kara jajircewa don ganin zaben ya fi haka nasara.
Tambuwal na jam’iyyar PDP ya bayyana hakan ne a yayin da jefa kuri’arsa ta zaben Shugaban Kasa da ‘Yan Majalisar Tarayya yana mai bayyana cewar idan da Shugaba Buhari ya sanyawa gyaran fuskar dokar zabe hannu da zaben zai fi haka inganci.
Gwamnan wanda ya jefa kuri’arsa a Tambuwal ya bayyana cewar Babban Zaben 2019 ya nuna Dimokuradiyar Nijeriya ta na kara samun ci-gaba a bisa ga yadda jama’a suka fito sosai a zabe.
Ya ce”Jama’a sun fito sosai kuma bisa ga abinda na gani za mu iya samun ingantaccen zabe a Nijeriya. Zabe yana gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da hayaniya ba.” Ya bayyana.
A Sakkwato jama’a sun fito sosai ba masaka tsinke domin sauke nauyinsu na zaben wadanda suke ra’ayin su shugabance su tun da sanyin safiya, da yawan jama’a na cikin layi tun kafin karfe 07:00 na safe. Kamar yadda wakinmu ya labarto mata sun fito zabe fiye da maza a zaben wanda har zuwa lokacin hada wannan rahoton yana gudana ba tare da tashin hankali ba.
A nasa bangaren Sanata Aliyu Wamakko na jam’iyyar APC ya bayyana fitowar jama’a a matsayin abin yabawa ya kuma bukaci masu zabe da su ci-gaba da bayar da hadin kai ga jami’an zabe domin gudanar da zabe lafiya.

Exit mobile version