Kamar yadda kundin ajiya na tarihin Kano da ake kira Chronicle ya nuna a shekarar (1890) ne babban tarihin Hausawa da yake na musamman ne idan har aka yi maganar kasar Kano domin tana daya daga cikin Hausa Bakwai, a shekarar 999 ce Bagauda wanda yake shi jika ne na Bayajidda (Abuyazidu), da shi ne ake alakanta shi ko da zarar an ambaci sunansa duk lokacin da aka yi maganar Hausawa.
An maida hedikwatar ta daga inda ake kira Sheme (zuwa Arewaci) wato inda birnin Kano yake a halin yanzu.
- Sabon Shirin Talabijin Ya Fara Gano Wasu Hanyoyin Kasuwanci A Nijeriya
- Abba Ya Mayar Wa Ganduje Martani Kan Bukatar Ya Koma APC
Sarki Gajemasu ya yi sarautar Kano ne daga shekarar (1095 zuwa1134) Malinke mutane masu da’awar addini su suka kawo addinin musulunci daga daular kasar Mali su suka kawo addinin musulunci Kano a shekarar 1340s, inda kuma Yaji shine Sarkin na farko da musulmi ya yi mulki ne daga shekarar (1349 zuwa 85).Ana ganin saboda Sarkin a lokacin musulmi ne shi yasa Zariya ta samu galaba a kan Kano kusan shekarar 1400, ta haka ne Sarki Kanajeji ya bar addinin musulunci, amma a shekarar 1450 masu gwagwarmayar yada addinin musulunci daga Mali suka sake dawowa daganan kumasai addinin musulunci ya sake dawowa da samun karfi.
A zamanin mulkin Sarki Dauda wanda ya yi mulki daga shekarar 1421 zuwa 38,Kano ta kasance ne a karkashin daular Kanem Borno (ta gabas),a zamanin mulkin Sarki Abdullahi Burja shekarar (1438 zuwa 52)an kulla hulda ta Kasuwanci da Borno.Fatauci ta Rakuma ya kawo bunkasar harkoki a karkashin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa daga shekarar(1463 zuwa 99),shine wanda ya fi bada gudunmawa daga cikin Sarakunan da suke Hausawa.Shi ya kafa Kasuwar Kurmi da Masallacin Jumma’a.Ya dawo da martabar gidan fadar Sarki wadda Sarakunan da suke Fulani da suka Mulki Kano suke amfani da ita.Ya yi yake-yake da Katsina garin da yake mil(92[ ko kuma kilomita 148] Arewa maso yamma ita abokiyar adawa ce da Kano idan ana maganar kasuwanci ko fatauci ta Rakuma inda ake bi ta hanyar Sahara mai yashi. A zamanin mulkin Muhammadu Rumfa aka sake dawowa da rubutu ta harshen Larabci ko kuma Arabic da kuma amfani da dokokin musulunci wajen mulkar jama’a.
Kano har ila yau ta kasance a karkashin daular Songhai zamanin mulkin Askia Muhammed na(1)a shekarar 1513 duk dai a cikin shekarar Kano ta kasance ta kasance karkashin Sarkin kasar Zazzau da take Kudu.Bayan Jukun ko Kwararrafa sun samu nasara a kanta tsakanin shekarun 1653 1671mutane daga kudu maso gabas,Katsina ta sa ba a ganin Kano a matsayin cibiyar kasuwanci,a shekarar 1734 ta sake komawa tana kai caffa ga Bornu.
A shekarar 1804 ne shugaban Jihadin jaddada musulunci na Fulani Usman dan Fodiyo, ya jagoranci wani harin da aka kai manyan Sarakunan Hauswa amma a shekarar 1807,aka samu cin Kano.Daya daga cikin almajiransa One of dan Sulaimanu shi ya zama Sarkin Kano na farko wanda ya gaje shi Ibrahim Dabo ya mulki Kano daga shekarar 1819 zuwa 46 daga gidan sarauta na Sullubawa har ya zuwa yanzu.