Ci gaba daga shafi na makon da ya gabata
Dalillan da Suka Karfafa Yakin Tattar
Tun da farko yana da kyau mu gano dalillan da suka karfafa bayyanar wadannan mahalukai masu kama da aljanu:
- Tattar sun tun faro kasar Musulunci a daidai lokacin da al’ummar Musulmi take cikin rauni a kowane bangare. Ga dai rarrabar kawuna wadda Allah ya hana mu. Ga talauci wanda ya faru a sanadiyyar yawan ambaliyar ruwa da aka yi shekaru ana yi wanda ya kawo wahalar abinci da tsadar rayuwa. Ga kuma ‘yan rigingimu da aka yi ta yi tsakanin Ahlus-Sunnah da tsirarun ‘yan Shi’ar da waziri ya daure masu gindi. Ga kuma karancin soja wadanda waziri ya kokkore su daga aiki yana nuna ma halifa cewa, akwai bukatar kula da tattalin arziki, don haka bai kamata a kashe kudaden gwamnati a kan soji ba.
- Halifan daular Abbasiyya na wancan lokaci mutumin kirki ne, mai son addini amma ba shi da ikon kome a hannunsa in ban da a birnin Bagadaza. Halifa kawai ya zama wani dodo wanda ba a ko iya ganin sa. An rufe shi cikin gida daga shi sai barori da
kuyangi. Bai san abin da duniya take ciki ba, kuma ita ma duniyar ba ta san abin da yake ciki ba.
- Kananan daulolin musulunci sun yarda da shugabancin Bagadaza kamar daular Ayubawa da ta Gaznawa da ta Khuwarizmawa da duk sauran kananan daulolin Musulunci in ban da daular ‘yan Shi’a ta Masar da ta Sufaye a Moroko. Su kam ba su
ma amince da halifa ba. Amma duka wadannan daulolin tare da amincewar su da gwamnatin Sunnah ta Bagadaza ba su zaune lafiya da ita. An yi ta yake- yake wadanda suka raunana kowane bangare.
Akwai wata dirama da ta faru a shekarar 529H a lokacin da sarki Mahmud ya yi yunkurin juyin mulki a kan Halifa Mustarshid, ya kuma ci nasara har da kama Halifa a hannu. Daga bisani kuma sarki “Sabjar” ya shiga tsakani bayan wani bore da
talakawa suka yi, ya sasanta har aka mayar da halifa a kan kujerarsa. Shekara daya bayan haka sai kuma sarki Mas’udu ya bayyana nasa tawayen, ya shelanta ya cire halifa ya nada kanin babansa Al- Muktafi, haka din kuma aka yi.
Bayan shekaru 11 aka samu wani rikici tsakanin halifa Muktafi da mai gidansa abinda ya jawo halifan ya sa aka rufe dukkan masallatai har tsawon kwana 3 ba a sallah cikin su. Bayan wasu shekaru 10 kuma aka sake wani ya mutsi tsakanin halifa da sarki Muhammad dan sarki Mahmud abin da ya jawo aka yi wata 2 ana zaman dar-dar a Bagadaza.
A takaice dai koda Tattar suka zo ba wani sarki da yake da karfi ko yake da cikakken hadin kai da wani in ban da Khuwarizm Shah. Don haka da gamawa da shi sai fili ya koma wayam; ba mai iya jayayya da su.
- A daidai lokacin da Musulmi suke cikin wannan rauni, sarakuna suka shagala da wasanni da sabon Allah, su kuma rundunar Tattar runduna ce kammalalliya. Duk inda suka zo basu bukatar kowa ya ba su ko igiyar daure rakumi. Suna da da wakai da
ra kuma da shanu wadanda suke cin namansu, da wadanda suke hawa kuma ba su bukatar a sauya masu dusa ko a ajiye masu kasari ko wani abinci, tonon kasa suke suna cin kwari da ciyawa da duk abin da ya samu. Ga su da yawan adadi wanda
mahaliccinmu kadai ya san iyakarsa. Ba su da tsoro, ba su ja da baya, ba su da jin kai ko miskala-zarratin ga mutane.
- Akwai wasu kura kurai da gangancin da sarakunan Musulunci suka yi musamman ma dai Khuwarizm Shah lokacin da ya kashe wasu ‘yan kasuwa da suka zo daga kasar Sin ba bisa ga wani dalili ba kuma ya kwace masu dukiya. A lokacin da wannan labari ya je ga Jinkizkhan sai ya aika masa wasika yana barazanar zai dau fansa, sai kuma Khuwarizmshah ya kashe jakadan ya sa aka aske gemun ‘yan rakiyarsa ya ce musu su je su kai labari.
Daga nan kuma sarki Khuwarizmshah ya je don yakar Tattar ya tarar sun fita zuwa Turkiyya don yaki da wani sarki ana ce masa Kashlokhan. Khuwarizm ya shiga garinsu, ya auka ma matansu da ‘ya’yansu amma bai bar garin ba sai da suka cim ma sa suka gwabza yaki mai tsanani. A cikin kwanaki uku suka kashe masa jarumawa Musulmi 20,000.
Tare da haka su ma sun yi hasarar rayuka ba iyaka. Tarihi ya ruwaito cewa, saboda yawan jinin da ya zuba na jama’a har zamewa dawa kai ke yi a cikinsa. 6. Kiristoci wadanda suka kasa karya lagon Musulmi a yakin Kuros (Crusade) ‘yan shekaru kadan a baya su ma sun taka rawa wajen kwadaitar da Tattar a kan kama kasashen Musulmi. Suka rinka nuna masu irin arzikin da ke cikin kasashen da saukin cin galaba a kansu.
A lokacin da Tattar suka kama kasashen Sham sun bayyana goyon bayansu ga kiristoci har su kan sa Musulmi su duka ma Kuros don wulakanta su.
- Akwai kuma tasirin munafukan Musulmi, ina nufin ‘yan Shi’ah. Tun a zamanin sarki Nasir dan sarki Mustadi’u bi amrillah wanda ya fi duk sarakunan daular Abbasiyyah dadewa (ya yi sarauta shekaru 47 daga 575H-622H) shi’anci ya fara karfi a cikin daular Musulunci saboda kisisinar da ‘yan Shi’ah suka yi ma sarki na aiko masa da takarda a sirrance rubuce da duk abin da ya yi a cikin dare, shi kuma sai ya yi tsammanin gaskiya ne Imaman Shi’ah sun sai gaibi kuma su ne ke fada masu sirrinsa. Alhalin kuwa yan leken asiri gare su daga cikin barorinsa. Wannan sarki – saboda shi’ancinsa – ya yi ta nuna ma Tattar goyon baya da ba su asirran Musulmi.
A kodayaushe yana aika masu wasiku. Sai na biyu shi ne sarkin garin Musil wanda ake ma lakabi da Al-Malik Ar- Rahim. Wannan sarki shi ma ya dade yana sarauta (tsawon shekaru 50), kuma dan Shi’ah ne da ya raya wasu al’adu da bukukuwa na kiristoci, ya kuma kulla alaka mai karfi da Tattar har da aurar da dansa Salihu ga ‘yar sarkin Tattar na wancan lokaci Hulako, duk da yake auren bai yi karko ba kuma ya haifar da rashin jituwa a tsakanin su amma dai ya ba da goyon baya da gudunmawa ga Tattar har ma mayakansa sun taimaka wajen yakar Bagadaza. Na uku shi ne uwa uba ga wannan al’amari, ina nufin Waziri Mu’ayyiduddin Muhammad Ibnu Ahmad Ibnul Alkami wanda ya hau mukamin waziri a zamanin sarki Musta’asim tsawon shekaru 14. Kuma ya yi iya kokarinsa ya daukaka shi’anci amma Ahlus- Sunnah suka rinjaye shi, sai ya bi ta hanyar hila da makirci kamar yadda muka riga muka fada.