Tarihin Tsohon Garin Dutsen Ɗan Baƙoshi

Wani mutum da a ke kira Ɗan Baoshi ne a ka ce ya kafa wannan gari mai tsohon tarihi na Dutsen Ɗan Baoshi shekaru da dama da su ka gabata.

Wasu sun ce daga Katsina ya ke, amma dai mafi shaharar zance shi ne Ɗan Baoshi Bamaguje ne, ɗan abilar Kutumbawa waɗanda su ke cikin mazaunan Kano na farko.

A haia babu takamaimen zancen da ke nuna garin ya girmewa Kano, amma dai ɗaukacin masu bada tarihin garin sun gamsu da cewa akwai alaar ut-da-ut tsakanin Aljana Mararraka da Aljana Tsumburbura wadda a ka bautawa a saman dutsen Dala ɗaruruwan shekaru da su ka gabata a birnin Kano.

An ce garin ya shahara a zamanin da, yana da ganuwa gagaruma, kuma ba a taɓa cin sa da yai ba, wanda ya sa mutane daga sassa daban-daban su ke niar gari domin shigewa ciki, saboda neman mafakar kamen bayi da yae-yae.

Wani abin da ke sanya mutane zuwa garin ma a zamanin-da shi ne shaharar Aljanna Mararaka, wadda a ka ce gidanta na saman babban dutsen Ɗan Baoshi, wanda ya ke a bayan ganuwar tsohon birnin.

Mutanen garin sun ce a baya a na ganin ta, a na kuma hurɗa da ita, a na yi ma ta yanka da hidimomi na wasu abubuwa, yayin da ita kuma ta kan taimaki mutane wurin samun biyan buatunsu na rayuwa.

Watakila itace silar zaman Ɗan Baoshi a wurin yana mai mata hidima kamar yadda Barbushe yayi ga tsumburbura, amma dai zuwa yanzu akwai karancin labari game da tsoffin abubuwa da suka faru tun asali a birnin.

Haka kuma, akwai labarin wurare masu ban mamaki a garin da har yanzu a na ganin su na da tasiri. Misali, an ce a baya duk baon da ya kusanci mazaunin Aljana Mararraka da ke saman katon dutsen, tofa sai ta bishi har gida ta halaka shi.

Don haka ya zamo al’adar mutanen garin hana duk wani bako kusantar wannan wuri. A cewarsu, ko a zamanin turawa akwai waɗanda suka ki-jin magana kuma suka mutu a sabili da kusantarsu ga wurin.

Akwai kuma wani wuri da a ka ce kafi ne irin na gari, da a kaiwa garin domin nemar ma sa kariya daga dukkan sharri, ance har gobe idan mutum ya taka wajen sai shauni ya kamashi iya tsawon wani lokaci.

Sunan sarautar garin Magaji, watakila tun bayan mutuwar Ɗan Baoshi ta fara, tunda a zamaninsa shine sarkin garin, watau dai kamar dai irin yadda ya faru ga magajin dala da magajin sontolo

Daga Sarakunan garin, wani da ake kira magaji Alu shine wanda har gobe akafi tunawa dashi, saboda kasancewarsa shine fulani na farko daya soma mulki a garin, da kuma hatsabibancin daya nuna zamanin mulkinsa.

Ance a lokacinsa akwai zama lafiya da kwanciyar hankali, kuma da kansa yake kama ɓarawo, domin daya ganshi yake gane shi. Sannan idan kaje gida kaganshi a kwance, kana zuwa gonarsa sai ka sake tarar dashi.

Zuwa yanzu dai, ganuwar garin ta rushe sai dai akwai shacinta, kuma babu ko ɓurɓushin murfin kofar da ake ɓame garin, amma tana iya yiwuwa akwai tsoffin kayan tarihi da ake ajiye dasu na mutanen da su ka gabata a garin.

Garin ya na nan a jihar Kano, arashin aramar hukumar shanono.

Exit mobile version