Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kara nanata cewa Kano za ta maimaita zaben shugaban kasa na shekarar 1993 inda jihar ta ki amincewa da danta, Marigayi Bashir Tofa, ta zabi MKO Abiola da gagarumin rinjaye.
“Hakan ya nuna kwarewar siyasa da hazakar ‘yan Kano. Mun zabi Cif MKO Abiola na jam’iyyar SDP, muka ki zabar Bashir Usman Tofa na NRC, sabida dukkanmu mun yi imani da hadin kan kasa da kuma cancantar dan takarar,” inji Gwamna Ganduje.
Ya bayyana hakan ne a yayin wani rangadin yakin neman zabe da yake yi tare da ‘yan takarar jam’iyyar APC, masu neman mukamai daban-daban a zabe mai zuwa, a lokacin da ya ziyarci hakimin Kibiya, Sunusi Abubakar Ila, bayan gudanar da taron yakin neman zabe da neman shawarwari a karamar hukumar Rano da Bunkure sannan kuma ya kwana a Rano, hedkwatar masarautar Rano tare da tawagarsa.
Gwamna Ganduje ya sake tunatar da ‘yan Nijeriya cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya goyi bayan ‘yan Arewa a lokuta daban-daban domin samun nasarar lashe zaben shugaban kasa, inda ya ce: “Tinubu ya taimaka wajen ganin Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AC. Ya kuma taimakawa Nuhu Ribadu wurin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ACN.”