A yau Asabar ne aka gudanar da zama na biyu na taro na uku, na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. Zaman da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping ya halarta.
Albarkacin kasancewar yau ranar bikin mata ta kasa da kasa, a madadin tawagar shugabannin taron, zaman ya mika fatan alheri ga mata daga dukkan kabilu, da dukkan bangarorin kasar Sin, da mata na dukkan kasashen duniya.
Bugu da kari, rahoton ayyukan zaunannen kwamitin NPC ya nuna cewa, ana shirin bitar dokoki 34 a shekarar nan ta 2025, wadanda suka hada da samar da wata doka, don inganta hadin kai da ci gaban al’ummar kasar. Ban da hakan, zaunannen kwamitin NPC, zai kuma karfafa binciken kafa dokoki masu nasaba da fasahohin AI, da tattalin arzikin dijital da sauransu.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp