Taron Gwamnonin Kudu: Taro Ne Na Marasa Kishin Nijeriya -Matasan Arewa

Taron

Daga Ibrahim Ibrahim,

Kungiyar cibgaban Matasan Arewacin Nijeriya, ta yi tir gami da takaicin yadda sakamakon taron Kungiyar Gwamnonin Kudancin Nijeriya ya kasance, maimakon su mayar da hankali wajen tattauna batun matsalolin kasar sai suka bige da batun komawar mulki zuwa kudu.

Kungiyar Matasan ta Arewa ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ta fitar wadda ta samu sanya hannun Shugaban Kungiyar na kasa, Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu, kuma aka rabawa manema labarai a Kaduna.

Matasan sun bayyana cewa, a fili yake Nijeriya na fuskantar manyan matsaloli da kalubale musanman akan harkokin da suka shafi tsaron kasar nan. To, zai zama abin mamaki idan ya zamana taron Gwamnonin Kudu ya kammala ba tare da tabo wannan magana ba sai suka kare da batun maganar komawar mulki zuwa Kudu. Tabbas a cewarsu, wannan taron da sukayi, taro ne na marasa kishin Kasar nan tamu ta Nijeriya.

A cewar Matasan, “Muna shawartar Gwamnonin na Yankin Kudancin kasar nan da cewa, kafin su kai ga batun komawar Shugabancin Kudu, kamata ya yi su mayar da hankali akan matsalolin dake addabar Jihohin su da tunanin lalubo hanyar magance su, amma ba kawai su bar Jaki su koma dukan taiki ba.”

Kungiyar ta Matasan Arewacin kasar nan, ta kara da bayyana cewa, “Kowa na sane da halin da Jihohin kudu suke ciki a halin yanzu, bangaren Kudu maso Yamma, wanda suka hada da fitinar Dan ta’addan nan Sunday Igboho, hakazalika a bangaren Kudu maso Gabas kuma, suma ba’a bar su a baya ba, musamman idan aka yi la’akari da fitinar ‘Yan Kungiyar Inyamurai masu fafutukar kafa kasar Yankin Biyafara, karkashin jagorancin Nnamdi Kanu da Kungiyar shi ta IPOB.”

A cewarsu, wannan babban matsalar ya kamata su fara batun magancewa, kafin surutun inda makomar Shugabancin Kasar nan zai koma. A cewar Kungiyar Matasan Arewa.

Exit mobile version