Ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS ya gudanar da zama a Talatar nan, a wani bangare na tsara ayyukan cikakken zama na 7 na kwamitin tsakiya na 19 na JKS, da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20.
Zaman ya amince da bude cikakken zama na 7, na kwamitin tsakiyar JKS na 19 a ranar 9 ga watan Oktoba a nan birnin Beijing, inda ofishin siyasa na kwamitin tsakiya zai ba da shawarar bude babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, a ranar 16 ga watan Oktoba dake tafe a birnin na Beijing. (Saminu Alhassan)