Tashar Wutar Lantarki Ta Ruwa Da Ke Karuma Ta Samar Da Kyakkyawar Makoma Ga Jama’ar Uganda

A karshen kogin White Nile dake tebkin Victoria na birnin Kiryandongo na arewacin kasar Uganda, masanan kamfani na 8 na samar da wutar lantarki ta karfin ruwa na kasar Sin, da ma’aikatan kamfanin dake wurin, suna kokarin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma a mataki na karshe, aikin da ya kasance mafi girma a wannan fanni a tarihin kasar.

An fara gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma a watan Disamba na shekarar 2013, bisa jarin kashi 15 cikin dari da gwamnatin kasar Uganda ta zuba, da kuma kashi 85 cikin dari da bankin shige da fice na kasar Sin ya samar da rancen kudi. Ana sa ran za a kammala gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa din a karshen shekarar bana wato shekarar 2018, tare da fara samar da wutar lantarki a hukunce, ta haka za ta kasance tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa mafi girma a yankin gabashin Afirka.

Kasar Uganda tana daya daga cikin kasashen da kowane dan kasar ke yi amfani da wutar lantarki mafi karanci a duniya. Yawan wutar lantarkin da mutanen biranen kasar Uganda bai wuce kashi 40 cikin dari bisa na adadin ’yan kasar ba, kuma yawan ta ga mutanen kauyukan kasar bai wuce kashi 6 cikin dari kacal ba. Haka kuma farashin wutar lantarki na kasar ya yi tsada, har ma mutane da dama na kasar ba su iya sabawa da shi, ta hakan an rage bukatun yin amfani da wutar lantarki na jama’ar kasar.

A hakika dai, kasar Uganda tana da fifikon albarkatu a fannin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa. Manajan mai kula da aikin tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma Xeng Changyi ya yi bayani cewa, a sakamakon sauri da yawan ruwan kogin Nile ba tare da samun babban canji ba, kana ba shi da lokacin cikar kogi da kuma lokacin kafewar kogi, ta haka ana iya samar da wutar lantarki ta karfin ruwan kogin yadda ya kamata ba tare da yin la’akari da lokacin kogin ba.

Xeng Changyi ya bayyana cewa, “Aikin tashar samar da wutar lantarki ta Karuma, aiki ne mafi muhimmanci da shugabannin kasashen Sin da Uganda suka sa kaimi ga gudanar da shi, wanda zai sa kaimi ga cimma burin kasar Uganda na samun ci gaba da wadata a kasar. Shugabannin kasashen biyu sun sa lura sosai kan aikin, kuma wannan muhimmin aiki ne dake cikin shirin samun bunkasuwa na shekarar 2040 na kasar Uganda.”

Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Uganda UEGCL, yana daya daga cikin kamfanoni masu gudanar da ayyuka a Karuma. Manaja mai kula da harkokin hadin gwiwa na kamfanin Simon Kasyate ya bayyana cewa, kamfanin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa na kasar Sin, abokin hadin gwiwa ne mai kyau a fannonin gudanar da ayyuka da horar da ma’aikata.

Simon ya bayyana cewa, “Yayin da ake gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa, wadda yawanta ya kai megawatt 600, kamfanin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa na kasar Sin yana son sauraron ra’ayoyinmu, da gyara shirin bisa hali mai dacewa, wanda hakan ke nuna kamfanin na daukar alhakin dake wuyansa. Mun yi imanin cewa, za a gama wannan aiki mai inganci yadda ya kamata bisa lokacin da aka tsara. Hakazalika kuma, kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya taimakawa kamfanonin samar da wutar lantarki na kasar Uganda wajen inganta karfinsu, musamman horar da ma’aikata a wannan fanni. A ganina wannan yana da muhimmanci sosai, domin bayan da aka gama aikin, ma’aikatanmu za su iya tabbatar da gudanar da ayyukan tashar samar da wutar lantarki yadda ya kamata. Ina tsammanin cewa, aikin Karuma zai kasance aiki mafi kyau a tarihin ayyukan gine-gine na kasar Uganda, za a ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakanin Uganda da Sin a fannin fasahohi na zamani, da kirkire-kirkire bayan da aka gama wannan aiki.”

Ban da sa kaimi ga inganta tattalin arziki, da sha’anin samar da wutar lantarki a kasar Uganda, aikin Karuma ya samar da ayyukan yi ga jama’ar kasar dake wurin. A halin yanzu, an samar da ayyukan yi ga ma’aikatan Afirka 6300 domin aikin Karuma. Khamisi Soniko yana daya daga cikinsu. Daga matsayin direba a shekaru 5 da suka gabata zuwa matsayin mataimakin manajan albarkatun kwadago a halin yanzu. Khamisi ya samu dukkan ingantuwa a fannin aiki, yayin da yake gudanar da aikin Karuma.

Khamisi ya fara yin mu’amala da bangaren aikin Karuma a watan Nuwanba na shekarar 2012. A lokacin, ya gama karatun jami’a, ya je neman aiki na Karuma. A sakamakon ba a fara gudanar da aikin Karuma ba, babu isassun ayyukan da ake bukata. Kuma babu aikin da ya dace da Khamisi sai aikin direba. Koda yake aikin direba ya bambanta da ilmin sarrafa albarkatun kwadago da Khamisi ya koya, amma Khamisi ya yi imani da kamfanonin Sin, da sha’anin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa sosai. Khamisi ya tsaida kudurin karbar wannan aiki, don haka ya zama ma’aikaci dake cikin tawagar farko ta kasar Uganda domin aikin Karuma.

A cikin shekaru 6 da suka gabata, Khamisi ya gudanar da aikin direba yadda ya kamata, tare da sauran ayyukan da ake bashi domin aikin Karuma. Bayan da aka daga matsayinsa sau biyu, a halin yanzu Khamisi yana aiki a ofishin albarkatun kwadago. Game da ayyukan da ya gudanar kan aikin Karuma a wadannan shekaru, Khamisi ya bayyana cewa, yana godiya ga kamfanin Sin da ya yi imani da shi, har ya taka hanya mai haske ta kokarinsa.

Khamisi ya bayyana cewa, “A yayin da nake aiki a Karuma, shugabannin bangaren Sin sun ba ni aiki bisa karfina, kana sun samar da damar karatu gare ni, ba a ba ni aiki daya ko biyu kawai ba. Ma’anar aikinsu ita ce za a inganta karfi na, ta yadda zan tinkari kalubale a nan gaba. Ina son bayyana cewa, kamfanin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa na kasar Sin, ya samar mini damar inganta karfina, da fadada ilmina, da daga karfin sarrafa ayyuka, kuma a nan gaba zan koyi ilmin albarkatu na digiri na biyu a jami’a.”

A ganin Khamisi, gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma, ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’umma dake wurin da aka gudanar da shi.

Khamisi ya bayyana cewa, “Hakika dai aikin Karuma ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki a kewayen nan. Kuma kudin shiga na jama’ar dake wurin ya karu. A shekarar 2013, yawan kudin haya na daki bai wuce Shilling 7000 a kowane wata ba, amma a yanzu ana iya samun sa kan Shiling 120000 a kowane wata. Matasan da suke sayar da ruwa a karamar motar bas, yanzu suna da gonakinsu, kuma sun fara yin ciniki.”

A hakika, aikin Karuma ya inganta kudin shiga na jama’ar dake wurin, kana ya dauki alhakin samar da gudummawa a wurin, kamar su gina gada a wani kauyen dake da nisan kilomita 4 daga wurin gudanar da aikin Karuma, da haka rijiya 10 a makarantun dake kauyuka na kewayen wurin, da gudanar da aikin bada jinya ba tare da biyan kudi ba a filin wasa na makarantar firamare ta Karuma, da samar da magunguna ga jama’ar dake wurin, da gina sabuwar kasuwa da dai sauransu. A ranar 8 ga watan Maris, bangaren aiwatar da aikin Karuma, ya samar da kudin karatu da rayuwa na shekaru 4 ga mata biyu masu karatu a makarantar midil, don taimakawa musu komawa makaranta.

Shugaban kwamitin garin Karuma Washington Chaya, ya kalli yadda aka gudanar da ayyukan a wurin, wadanda su ma suka kawo moriya gare shi. Ya ce, “Lokacin da aka fara gudanar da aikin Karuma, kamfanin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ya yi alkawari ga gwamnatin kasar Uganda cewa, zai taimakawa bunkasa zamantakewar al’umma a kasar, kamar ta gina tashar bada jinya, da samar da kudin kyauta ga mutane masu fama da matsaloli, da gina makarantu da dai sauransu. Mun yi mu’amala mai kyau tare da kamfanin, domin a hakika kamfanin ya gudanar da ayyuka da dama gare mu. Ban da ayyukan da na fada dazu, sun taimakawa gina ayyukan more rayuwa a wurin, ciki har da haka rijiya, da samar mana ruwa, da samar da abubuwan gine-gine, da kuma gina hanyoyin motoci. Haka kuma, ana samar da wutar lantarki a wuraren da ba su da ita a lokacin. A ganina wannan aiki ya samar mana moriya da dama.”

A tsakiyar babban ginin bangaren gudanar da aikin Karuma, akwai kalmomi a wani allo dake cewa, “kamfanin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa na Sin da jama’ar kasar Uganda, na yin kokari tare don samar da kyakkyawar makoma”. Kamar yadda ake bayyanawa, an gama gina kamfanin sarrafa iskar gas, da hanyoyin jingila na kasar Tanzania a shekarar 2015, da gina hanyoyin jiragen kasa dake tsakanin Addis ababada da Djibouti a shekarar 2016, da hanyoyin jiragen kasa dake tsakanin Mombasa da Nairobi. Kana kuma za a gama aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Karuma a bana. Ana iya ganin cewa, gwamnatin kasar Sin da jama’arta, suna son yin kokari tare da kasashen Afirka, da jama’arsu, wajen gina ayyukan more rayuwa a tsakanin Sin da Afirka, tare da samar da kyakkyawar makoma. (Marubuta: Zhou You & Ahmad Haji, ma’aikatan sashen Swahili na CRI; Mai Fassarawa: Zainab Zhang, ma’aikaciyar sashen Hausa na CRI)

Exit mobile version