Connect with us

MATASAN ZAMANI

Tasirin Kafafen Sadarwa Na Zamani Ga Rayuwar Matasa Da Al’umma (II)

Published

on

Haka zalika, yau dumbin matasa sun tattare sun komai sun ba wa waya muhimmanci, sun fi son tattaunawa da abokansu na (Social Media) fiye da abokansu na zahiri, sannan kuma su na shafe lokaci mai tsawo fiye da lokacin da su ke ba wa iyalai da ‘yan uwansu. A duk lokacin da matasa su ka farka daga barci abu na farko da su je farawa da shi, shi ne bude shafukansu na sadarwa haka zalika kafin su kwanta barci ma shi su ke lekawa a kowacce rana.

Haka nan a wurararen aiki matasa kan bata lokutan aiki da dama a kan (Socia Media) su na kalle-kalle da duba labarai da rahotanni da tattaunawa da abokai. (Social Media) ta zama kamar misalin mashayi da kayan shaye-shaye in dai bai sha ba to babu nutsuwa da zaman lafiya a wannan lokaci. Ba a maida hankali akan aiki yadda ya kamata matasa su na ba wa kafafen sadarwa na zamani kaso mai yawa na lokutan aiki.

 

Sannan matasa ba sa takaita yawan Comment (sharhi) da Like (jinjina) da Post a kullum su na yin komai domin ganin cewar a kullum ba su gajiya ba. Sannan wasu daga cikinsu su na daukar hotuna da bidiyo a wuraren zama da cin abinci na alfarma su yada a shafukan sadarwa na zamani duniya ta gani da sunan rayuwarsu domin su burge al’umma alhalin kuwa ba haka su ke ba a rayuwa ta zahiri. Kuma akwai wadanda a kowane lokaci su na kan soshiyal media su na kashe kudadensu wajen sayen data domin kawai su dora abubuwa duniya ta gani su samu suna ko wata daukaka. Lamarin da hatta masana halayyar Dan Adam sun tabbatar da cewar ya na iya haifar wa Dan Adam matsaloli kamar depression (kunci).

Daga cikin illolin na (Social Media) dai akwai hatsari da kasada da kuma laifuffuka da ake tafkawa a cikinsu. Babban laifi da ke zuwa a cikin zukatan jama’a shi ne kutse da wasu batagari kan yi a cikin shafukan sadarwar jama’a. Akwai dumbin jama’a da su ke boye hakikanin bayanan kansu a wadannan shafuka na sadarwar zamani ba sa bayyana hakikanin yadda su ke.

A ya yin da ake samun masu boye bayanan kansu, ana kuma samun wadanda su ke bayyana komai na rayuwarsu tun daga kan makarantun da su ka yi zuwa addinin da su ke bi har zuwa wuraren aikunsu, ta yadda duk inda su ke da duk inda za su je sai sun bayyana, a irin wannan yanayi mutanen da su ke da manufa mummuna a kan mutum farkon abin da za su fara dubawa shi ne shafinsa na (Social Media) domin gano yadda za su same shi su yi masa ta’addanci.

Dadi da kari, (Social Media) kan haddasa wa Dan Adam matsaloli ta fuskar lafiya kamar matsalar ido da kuma karancin motsa jiki da yawan zama wuri guda tare kuma da ciwon zuciya da cutar suga da matsalar yawan bugawar jini da rashin son zama cikin jama’a.

Wannan kuma kan haifar wa Dan Adam matsalar a rayuwarsa ta gaba duba da cewar kiyaye dangantaka na daga cikin rukunin tattaunawa. Sannan kuma ana yada labarai na karya wadanda ba su inganta ba, kuma su na iya taba dangantakar mutum da mu’amalarsa da al’umma da ‘yan uwa da masoyansa idan aka yada wani labari na karya a kansa.

 

Sannan daga cikin cigaban da kamfanoni su ka samu, su na bude shafukar sadarwar zamani wajen yada kayayyakinsu ta hanyar ma’aikatansu to idan ya kasance wani daga cikin ma’aikata ya aikata wani abu wanda ya janyo wa kamfanin bakin fenti, to kamfanin zai iya korarsa nan take.

Sanna sabbin kafafen sadarwa na zamani su kan taimaka wajen taba kima da darajar mutum ta yadda mutum zai watsa wani abu da tunanin gamsar da al’umma amma hakan sai ya batawa mutane rai su kuma rika ganinsa a reni ko wani abin dariya. Misali wasu su na sanar da wani al’amari da ya same su kamar mutuwar wani nasu ko rashin lafiya amma sai wasu su mayar musu da sakon jaje mai dauke da nuna farin ciki da taya murna. Sannan duk abin da ya dame ka kuma ka rubuta jama’a su ka jajanta maka to fa shikken an jimawa da zarar ka saki wani sakon nan za su koma, sannan daga cikin dumbin wadanda su ka jajanta maka kadan ne za su iya zuwa su jajanta maka a rayuwa ta zahiri.

 

Akwai wani manazarci da ya ke cewa “ina tsoron ranar da fasahar sadarwar zamani za ta raba haduwar al’umma wuri guda” duba da cewar kusan komai ya koma kafafen sadarwa na zamani. (Social Media). Hanyar da za ka sadaukar da lokacinka ka ga komai da ya ke faruwa a duniya ka na zaune kafa ce mai matukar gamsar da mutane da kayatar da su da kuma shiga rai matuka sannan kuma kafa ce mai tarin hatsari da kalubale kasancewar a sake take ba kaidi. Wadanda su ka kirkiro da wadannan kafofin sadarwa na zamani ba su taba tunanin cewar kafofin za su zamto yadda su ke ba a yanzu haka duba da yadda kafofin su ka samar da nakasu ta fukar mu’amala da ayyukan laifi da kuma samar da cigaba ta fuskoki da dama ga rayuwar matasa.
Advertisement

labarai