Dakta Aliyu Ibrahim Kankara" />

Tasirin Wakokin Mata Ga Wadanda Aka Yi

Ma Su Na Dokta Mamman Shata Katsina

Dandano Jiran Rabo

Mata na da matukar rawar da su ke takawa a rayuwar Dan Adam ta fannoni da dama. A fadin kasar Hausa kaf wakokin mata na mawakan baka sun yi tasiri kwarai ta fuskar bunkasa tattalin arzki da ci-gaban siyasa ko wasu manufofin gwamnati da kuma nishadantar da al’umma. A wannan takarda, an duba yanda wasu zababbun matan da Shata ya yi ma waka suka kalli wakokin, ba wani da ya ji ko ya san wakokin daga bayan fage ba. Takardar ta kuma duba yanda matan suka dauki kawunan su, da yanda rayuwarsu ta kasance bayan an yi masu wakokin, da kuma tasirin wakokin ga rayuwar su, gami da amfanin su dare su, idan akwai. Hanyoyin da aka bi wajen tattara bayanan takardar ba su wuce littattafan Shata Ikon Allah (2006) da kuma Shata: Mahadi Mai Dogon Zamani (2013, 2018) da aka yi amfani da shi, na tattara bayanan hirarrakin da aka yi da matan da takardar ta zabo a tsakanin 1993 zuwa 2018. Hanyar binciken ta kuma tattaro wasu intabiyu da aka yi da wasu jama’a can daban da suka taimaka wajen tada takardar. Sakamakon binciken ya gano cewa wakokin sun yi wa wadanda aka yi ma su amfani da tasiri kwarai da ainun. Ma’ana wakokin sun kara masu martaa da daukaka a cikin al’umma.

Gabatarwa

Saboda salon gwanancewa ma, a wakokin matan ma babu inda Dokta Mamman Shata Katsina bai tabo ba (Bangul, 2000; Kankara, 2013, Boss, 2015; 2018a). Kamar yanda Shata ya bambanta da sauran mawaka a irin yanayi da sigogin wakokin sa, to hakama ga wakokin sa na mata (Juma, 1995; Jinjiri, 1998; Gilashi, 2000; Bature, 2000; Babban Duhu, 2014).

Mata sun taimaka ma Shata wajen habaka wakokin sa don da su ya fara karyawa a matsayin ‘yan amshin sa ko abokan wake-waken sa tun ma kafin ya guguta ya zama abin tsoro (Falgore, 1999; Danhausa, 2006; Iya, 2008)  Don haka alakar Shata da mata tun farkon zamanin wakar sa kakkaura ce, mai girma ce (Nasara, 1999; Yalwa, 1999; Nana-Dankwara, 2000; Binta, 1999; 2001; 2002) Bincike ya nuna cewa mata masu zaman kan su sun fi samun kaso mai yawa daga cikin wakokin mata na Shata, musamman saboda alakar su da jam’iyyu a jamhuriyya ta farko da ta biyu, da kuma irin rawar da su ka taka a cikin siyasun. Sakamakon binciken ya nuna cewa kasaita da tagomashi da mafi yawancin matan da Shata ya yi ma waka ta sanya ya yi masu wakoki. Sakamakon ya kuma gano cewa jam’iyyar NPC ta taimaka wajen daga wasu matan da su ka yi ma ta hidima matuka, wanda hakan ya sa Shata ya yi masu wakoki (Adama, 2000; Tuni, 2009; Barka, 2013)

In da duk makadin ya sauka, da an gama cin kasuwa da dare sai a sa wasa a dandali, ‘yammata da samari su taru mawakan Asawwara da makadan su su zo, ga kuma Shata gefe guda, shima ya shigo cikin fage, to nan zai samu makadan da ma’amsan, idan ya gama wasan nan zai tafi ya barsu (Bangul, 2003). Har ma ga shi yana fadi a wata Asawwara. Da an ce wance ta wuri kaza zabaya ce sai Shata ya so ya ga ko wacece wannan zabaya, zai so ya ji nata ilimin wakar. Tsakanin ‘Yantumaki da Dutsin-ma (ana tsammani Danmusa ne) an yi wata wai ita zabaya ‘Yar Kado, bamaguza ce don haka Allah ya yi mata Hausa. Ya taba zuwa ya same ta don har kawance sun yi. Mene ne kawancen da, a kawo wa mutum alkaki ko zuma ko gasassar kaza ko a baka kyautar luru (bargo da ake yin lage da shi, akan ba da shi kyauta don wata bajinta da mutum ya yi) Ita kuma mace ta ba namiji kyautar cunku., cunku kuma wani abu ne da mata ke ratayawa a wuya a matsayi ado (Salisu, 2005). Shata kan yi bakin zabayoyi a Musawa, shi ke saukesu, harma a hadasu gasar rawa da waka, ya kuma samu galaba a kansu. Tun a wannan wakati Shata ya fahimci muhimmancin mata a rayuwar wakarsa. Don haka bai yada su ba (Shata, 1994; Shata, 1997; Dan Amare, 1999) Doka, 1998) Garba-Sudan, 1999) Hadiza, 1999) Hurera, 1999) Halima, 2002) Hassana, 2014) Abdullahi, 2013)

A cikin littafin Shata Mahadi Mai Dogon Zamani an kawo akalla jerin gwanon wakokin mata kimanin 481.

Takardar ba ta tabo sauran matan da akan ambata a waka ba, ko da kuwa an taba cin karo da su aka yi hira da su, kamar su Iya Binta Bakori, Abun Na-Borno, Hajara Gigama Musawa, Zabaya Rabin Bature, Binta Tambai ‘yar gwamna da Asabe Dilla Ketare (da akan ambace su a wakokin Asawwara) (Gigama, 1999; Kumbula, 1997) Duk wadda Shata ya yi ma waka sai an yi rububi da dokin ganin ta. Cikin 1955 Shata ya tafi Daura sallar Gani da Indo A’I Kyaftin. A wani benen kasa mai hawa daya aka sauke ta. Wanshekare da safe jama’a suka rika yin tururuwa suna kallon ta (Doka, 1998).

A waka Shata ba ya da bango, ba ya da iyaka; ba sarakuna ba, ba talakawa ba, kai hatta mata masu zaman kan su, duk da yake sana’ar su abin kyama ce bai nuna ya kyamace su ba, duk da yake a wasu lokuta ya yi wakokin (1956, 1962) yi masu gargadi da su yi aure su dana karuwanci (Zuwaira, 1999; Yalwa, 1999; Dikke, 1999; Kankara, 2010c; Kankara, 2012).

Exit mobile version