Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya gargadi Nijeriya game da karbar duk shawarwarin da cibiyoyi na Bretton Woods ke bayarwa, musamman Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF).
Jega ya yi wannan gargadin ne a ranar Laraba a cikin lakcar da ya gabatar a taron shekara-shekara na Daraktoci na 2024 mai taken, “Shugabanci nagari, shi ne mafita ga shirin habaka tattalin arziki,” wanda Cibiyar Daraktocin Nijeriya ta Chartered (CIoD) ta shirya.
- EU Za Ta Janyowa Kan Ta Lahani Sakamakon Kakaba Karin Haraji Kan Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin
- Mene Ne Burin Amurka Wajen Sake Yada Jita-Jitar “Barazanar ‘Yan Leken Asirin Kasar Sin”
A cewar Jega, duk da cewa yana da kyau a samu bayanai daga IMF da sauran su, amma dole ne gwamnati ta yi taka tsantsan don guje wa jefa kasar cikin manyan matsaloli.
Jega ya kuma yi kira da a sake fasalin tsarin daukar shugabannin kasar, inda ya bayyana cewa, babban kalubalen da ke gaban Nijeriya shi ne, yawancin shugabanninta ba su shirya wa jagorancin ba.