• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tattalin Arziki: Gwamna Lawal Ya Nemi Hadin Gwiwar Masu Zuba Jari Na Kasashen Afirka A Taron AFREXIM A Kenya 

by Sulaiman
11 months ago
Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin haɗin gwiwar ci gaba na gaskiya da adalci da za su amfani zamantakewa da tattalin arzikin jihar.

 

Gwamnan ya wakilci Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya, kuma ya kasance babban baƙo a taron ƙara wa juna sani na Haɗin Gwiwa na Ƙasashen Afirka karo na huɗu, wanda aka gudanar ranar Litinin a otel ɗin Swiss Grand Royal da ke garin Kisumu ta ƙasar Kenya.

  • An Kama Dillalin Safarar Makamai Dan Aljeria A Zamfara 
  • Xi Ya Bukaci A Aiwatar Da Kudurin Kwamitin Sulhun MDD Kan Batun Palastinu

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, taron da aka fara daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Nuwamba, Shugaban Ƙasar Kenya, Dr. Williams Ruto ne ya buɗe taron.

 

LABARAI MASU NASABA

Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

Sanarwar ta ƙara da cewa, taken taron na AfsNET shi ne “Yin amfani da AfCFTA don Samun Ɗorewar Cinikayya da Zuba Jari: Hanyar Ci Gaba ga Ƙasashen Afirka.”

 

Gwamna Lawal, wanda ke gabatar da saƙon fatan alheri a madadin Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya, ya ce taken taron na AfsNET na bana ya yi daidai da muradun ci gaban gwamnatocin ƙasashen Afirka. “Taron na ƙalubalantar mu da mu daidaita dabarunmu da albarkatunmu don buɗe damar kawo sauyi a harkar Cinikiyyar Ta Gaskiya d Adalci A Afirka (AfCFTA).

 

“A Nijeriya, mun fahimci muhimmiyar rawar da ƙananan gwamnatocin ƙasashe ke takawa wajen tafiyar da harkokin kasuwanci, zuba jari, da ci gaban tattalin arziki. Jihohinmu 36 cibiyoyi ne na tattalin arziki daban-daban, kowannensu yana da rawar da yake takawa ta musamman da ke ba da gudunmawa ga tattalin arzikin ƙasa.

 

“Ana iya ganin babban misalin hakan a shirin Agro-Allied Industrial Zone ta Jihar Kaduna, shirin haɗin gwiwar gwamnati da ɗaiɗaikun jama’a da aka tsara don inganta noma tare da sarrafa anganin gona don fitarwa zuwa waje.

 

“Wannan aikin yana nuna yadda masu mulki za su iya amfani da albarkatun cikin gida da kuma tsarin AfCFTA don haɓaka ƙimar kasuwanci da faɗaɗa damar kasuwanci a duk faɗin Afirka. Hakazalika, yankin AfCFTA na Lekki ya zama abin koyi na samar da masana’antu da kuma jawo hannun jari kai tsaye daga ƙetare a jihar Legas. ”

 

A wajen taron tattaunawa kan samar da mafita mai ɗorewa ga ci gaban yankin Afirka, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, haɗin gwiwa ne zai kawo daidaito a bangaren ci gaban tattalin arziki.

 

“A matsayina na gwamna a yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya, tare da haɗin gwiwar wasu gwamnoni shida, mun ƙirƙiro Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma don bayyanawa tare da daidaita manufofin da za su samar da haɗin kan yankin don samun ci gaba mai ɗorewa. Wannan ya riga ya fara samar da sakamakon mai kyau a yankin.

 

Dangane da batun tsaro, Gwamna Lawal ya jaddada cewa, in ba tare da ingantaccen tsarin muhalli ba, gwamnatoci ba za su iya samar da ayyukan jin daɗin jama’a yadda ya kamata ba kamar ilimi, kiwon lafiya, daidaiton jinsi, kawar da rashin daidaito, da samar da ayyukan dogaro da kai ga maau ƙaramin ƙarfi, waɗanda su ne muhimman abubuwan da ake buƙata don ci gaba mai ɗorewa.

 

“Tsarin mulki ya taƙaita ƙarfin Gwamna ta fuskar samar da tsaro ga al’ummar da yake mulka; duk da haka, mun yi namijin ƙoƙari wajen ganin mun tabbatar da cewa muhallinmu ya kasance cikin kwanciyar hankali ta hanyar kafa Rundunar Kare Al’umma (CPG), wadda ta daƙile matsalar rashin tsaro da ake fuskanta kafin zuwan gwamnatina.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani
Manyan Labarai

Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus
Manyan Labarai

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Next Post
Yadda Amfani Da Karen Mutum-mutumi Da Jiragen Ruwa Da Motoci Masu Sarrafa Kansu Ya Kara Fito Da Ci Gaban Fasahar Kasar Sin

Yadda Amfani Da Karen Mutum-mutumi Da Jiragen Ruwa Da Motoci Masu Sarrafa Kansu Ya Kara Fito Da Ci Gaban Fasahar Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025
Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo

Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo

October 19, 2025
Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani

Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani

October 19, 2025
Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

October 19, 2025
JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.